Wasu ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Tsanwa dake ƙaramar hukumar Batsari a Jihar Katsina inda suka kashe mutane akalla 20, yayin da suka cinnawa gidajen mutane wuta da kuma kwashe dabbobin su.
Shaidun gani da ido sun ce maharan akan babura dauke da makamai sun kai hari ne goshin magariba inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, suka kuma cinnawa gidajen mutane wuta da kuma kwashe dabbobin jama’a.
Wani mazaunin kauyen da ya sha da kyar yace sun shaidawa jami’an tsaro lokacin da ake harin amma har barayin suka tafi babu wanda ya kai musu dauki.
Wata majiya tace bayan kai harin Tsanwa, Yan bindigar sun tafi zuwa kauyen Yar Lumo inda suka kwana suna harbi da kade kade sakamakon nasarar da suka samu.
Kakakin rundunar Yan Sandan Jihar Gambo Isa yace kwamishinan Yan Sanda Sanusi Buba ya ziyarci kauyen domin ganewa idan sa abinda ya faru.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin da suke fama da matsalar tsaron Yan bindiga dake kai hari garuruwa suna kashe mutane ba tare da kaukautawa ba.
Yunkurin gwamnatin jihar na sulhu da wasu bangarorin Yan bindigar ya rushe ganin yadda suka sake daukar makamai bayan sun yi alkawarin daina kai harin.