Tarihi: IBB ya cika shekaru 80! Abubuwan da ya kamata ku sani game da shi

38

Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida, shi ne tsohon shugaban Tarayyar Najeriya na 8, kuma tsohon sojan Najeriya mai ritaya wanda ya yi aikin soja tun daga matakin sakan laftanar har zuwa janar.

Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida mutum ne ɗan kishin ƙasa, jarumi, mai basira, hangen nesa, sannan kuma mai fasaha da kuma ƙwazo wajen aiki, ya bada gudunmawa mai gwaɓi a fannin aikin soja tun daga kwamanda har ya zama shugaban ƙasa.

Ya bada gagarumar gudunmawa wajen kasantuwar Najeriya a matsayin ƙasa ɗaya, ta hanyar daƙile yunƙure-yunƙuren juyin mulki da dama tun kafin zamowarsa shugaban ƙasa. Shi ne sojan da ya hau kujerar shugabancin Najeriya ta hanyar juyin mulkin da ba a zubar da jini ba; mutum ne da ya baiwa Najeriya da ‘yan Najeriya gudunmawa tun daga shekarar 1964 har zuwa 1993 a matsayin Soja, sannan kuma ya ke ci gaba da bada gudunmawa ta fannoni da dama na rayuwa.

Ya kafa hukumomin da har gobe suke bada guraben ayyukan yi a Najeriya kamar irinsu hukumar kiyaye haɗɗuran kan titi (Federal Road Safety Corps), hukumar samar da ayyukan yi (National Directorate of Employment), da sauransu.

Ibrahim Badamasi Babangida

Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida, bayan kasancewarsa soja, kuma ɗan siyasa daga baya, malamin addinin Musulunci ne wanda ya ke gudanar da fassarar alƙur’ani daga gidansa a cikin watan azumi mai albarka

Takaitaccen Janar Ibrahim Badamasi Babangida

An haifi janar Babangida ranar 17 ga watan Agusta na shekarar 1941 a garin Minna na jahar Neja.

Ya yi karatu a makarantar soji ta India a shekarar 1964, makarantar horas da sojoji ta Royal Armoured Centre ta Ingila daga 1966, kwalejin sojoji ta Jaji a shekarar 1977 da kuma makarantar sojin ruwa ta Amurka a shekarar 1980.

A shekarar 1962 ya shiga aikin soji inda yai aiki a gwamnatin sojin janar Obasanjo. Ya taka rawar gani a juyin mulkin 1976.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi aure ranar 6 ga watan Satumbar 1969 ga Maryam wadda Allah ya yiwa rasuwa ranar 27 ga watan Disambar 2009. Janar Babangida na da ‘ya’ya 4 biyu maza biyu mata.

Juyin mulkin shekara ta 1985

Ranar 27 ga watan Agustan shekarar 1985, sojoji karkashin jagorancin janar Ibrahim Badamasi Babangida suka hambarar da gwamnatin janar Muhammadu Buhari a wani juyin mulkin da ba’a zubda jini ba.

Babban dalilin da sojojin suka bayar na hambarar da gwamnatin janar Muhammadu Buhari shi ne na dagewar da yayi na cewa sai ya gudanar da bincike a ma’aikatar tsaron kasar game da zarge-zargen da ake na wasu kwangiloli da aka bayar a ma’aikatar.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida da marigayi Janar Sani Abacha

Wasu na ganin da a ce an gudanar da bincike to kuwa da an samu dayawan manya-manyan sojojin da hannu, wadansu sune suka hada juyin mulkin.

Janar IBB kamar yadda ake kiransa ya hau mulkin da zummar kawo karshen take hakkin bil’adama da ake zargin gwamnatin Buhari da yi tare kuma da mika mulki ga farar hula a shekarar 1990.

Sai dai kuma wasu na ganin take hakkin dan adam din ya ma fi kamari a lokacin mulkinsa.

A lokacin mulkin janar Babangida aka kaddamar da shirin tada komadar tattalin arziki wato Structural Adjustment Program ko SAP a takaice a shekarar 1986, kamar yadda hukumar bada lamuni ta duniya wato IMF da Bankin Duniya suka ba gwamnatin shawarar yi domin farfado da tattalin arzukin kasar.

Kuma wannan shiri a iya cewa yayi tasiri tsakanin shekarar 1986 zuwa da 1988 a lokacin da aka samu bunkasar tattalin arziki.

A lokacin mulkin janar Ibrahim Badamasi Babangida ne Najeriya ta zama cikakkiyar mamba a kungiyar kasashen musulmi wato OIC.

Ranar 22 ga watan Aprilun shekarar 1990 wasu sojoji karkashin jagorancin Manjo Gideon Orkar sukai kokarin kifar da gwamnatin IBB.

A lokacin da sojojin suka yiwa fadar shugaban kasar kawanya, janar Babangida yana ciki, amma dai ya samu ya sulale ta wata barauniyar hanya ta bayan gidan.

Gudunmawar Gwamnatinsa

Marubuta da dama sun yi rubuce-rubuce masu tarin yawa dangane da nagarta da kyawawan manufofi da kuma gudunmawa mai gwaɓi da wannan gwamnati ta shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ta bayar a zamanin mulkinta duk da irin matsaloli ta ci karo da su musamman a ƙarshen mulkinta.

Gwamnatin shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ta yi ƙoƙarin da dukkan gwamnatocin da suka gabace ta basu yi ba dangane da haɓɓaka tattalin arziƙin Najeriya, duk da cewa ɗaiɗaikun mutane sun fuskanci rashin kuɗi amma tattalin arziƙin ƙasar nan ya ci gaba. Kaɗan daga cikin irin waɗannan gudunmawowi akwai:

 1. Shigo da jama’a harkokin mulki: Duk da kasancewar gwamnatin shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ta soja; wacce ake yiwa kallon kama-karya, ta tuntuɓi jama’ar Najeriya dangane da ra’ayinsu kan karɓar lamuni daga asusun bada lamuni na duniya (IMF) wanda aka fara tattaunawa tun gwamnatin farar hula ta shugaba Shehu Shagari, sannan kuma gwamnatin soja ta shugaba Muhammadu Buhari ta ɗora.

A nan, waɗanda basu yarda da karɓo bashin ba su suka fi rinjaye, saboda haka sai shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ya janye maganar.

 1. Fito da tsarin ‘Structural Adjustment Programme’, wato SAP a taƙaice. Nuna rashin amincewar ‘yan Najeriya kan karɓo waccan bashi, sai shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ya fito da wannan shiri, dan ingantawa tare kuma da haɓɓaka tattalin arziƙin Najeriya. Wannan tsari na SAP, yana da manufofin da suka haɗa da:
 • Rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen bayar da tallafi kan albarkatun mai.
 • Samar da hanyoyin dogaro da kai; wato ya zama ita ƙasar ta dogara da kanta ta fuskanci samar da wasu abubuwa na more rayuwa saɓanin dogaro da wasu ƙasashen ƙetare.
 • Toshe giɓin da ake samu a kasafin kuɗin Najeriya.
 • Rage dogaro da shigo da kayayyaki da kuma albarkatun mai a matsayin babbar hanyar samun kuɗaɗen shiga.
 • Haɓɓaka nagartar masana’antu masu zaman kansu dan su zama masu samar da ci gaba.
 • Inganta harkokin masana’antun gwamnati ta hanyar sayar da kadarorin gwamnati dan su koma masu zaman kansu, wanda wannan shi ne ya kafa tubalin sayar da kamfanin sadarwa na Najeriya (NITEL) wanda yanzu ya zama kafa ta samun kuɗaɗen shiga da kuma samun kafofin sadarwa da dama ta hanyar baiwa kamfanonin sadarwa irinsu MTN, glo, da sauransu damar zuba jarinsu kamar yadda ake iya gani.

 1. Ƙiroƙiro sababbin jahohi guda goma sha ɗaya: Babbar manufar wannan shiri ita ce kusanta gwamnati da jama’a da kuma kusantar da jama’a ga gwamnati da kuma uwa-uba samar da guraben ayyukan yi.
 2. Kafa Hukumar Haɓɓaka Aikin Gona da Albarkatun Ƙasa (Nigerian Agricultural and Land Deɓelopment Authority (NALDA)), ƙarƙashin wannan hukuma aka ƙirƙiri hukumomi masu yawa a faɗin tarayyar Najeriya waɗanda suke kula da inganta harkokin noman rani ta hanyar samarwa tare kuma da kula da fadamu.
 3. Kafa Hukumar Inganta Rayuwar Matan Karkara (Better Life for Rural Women).
 4. Hukumar Wayar da Kan Jama’a Game da Farfaɗo da Tattalin Arziƙi, Dogaro da Kai, da Kuma Adalci (Mass Mobilisation for Economic Recoɓery, Self-Reliance and Social Justice (MAMSER) a watan Agusta na shekarar 1987.
 5. Kafa Kwamitin Sabunta Tsarin Mulki (Constitution Reɓiew Committee) Satumba 1987.
 6. Kafa Hukumar Zaɓe (National Electoral Commission (NEC), Disamba 1987.
 7. Dawo da babban birnin tarayya zuwa Abuja a shekarar 1991.
 8. Kafa Hukumar DEFFRI, hukumar da ke kula da harkar abinci, gina hanyoyi da kuma sauran kayan more rayuwa a yankunan karkara.
 9. Hukumar Samar da Ayyukan yi (National Directorate for Employment (NDE); hukuma ce da ta riƙa koyar da sana’o’i ga ‘yan Najeriya dan a samu ayyukan yi. Wannan hukuma tana da cibiyoyi da makarantu da har ta kai ga akwai motoci masu tsarin makaranta da suke shiga ƙauyuka dan koyar da sana’o’i.
 10. Hukumar Kiyaye Haɗɗuran Kan Titi (Federal Road Safety Commission (FRSC), tabbas wannan hukuma tana bayar da gudunmawa ta fuskokin da suka haɗa da samar da ayyukan yi, tara kuɗaɗen shiga ga gwamnati, rage afkuwar haɗɗura ta hanyar tuƙin ganganci, ɗaukar majinyatan haɗari zuwa asibitoci, da sauransu.
 11. Bankin Al’umma (Peoples Bank), banki ne da aka kafa shi da nufin taimakawa ƙananan ‘yankasuwa su samu rance ba tare da sun bayar da fansa ba. Wannan banki yanzu babu shi.
 12. Bankin Kwamuniti (Community Bank).
 13. Inganta Albashin Ma’aikata.
 14. Ɗaukaka darajar Najeriya daga matsayin mai saka ido ya zuwa cikakkiyar mamba a Zauren Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi (Member Organization of Islamic Conference (OIC), a watan Janairu na shekarar 1986.
 15. Kafa Kwamatin Kula da Miƙa Mulki ga Hannun Farar Hula.
 16. Ya ƙirƙiri jama’iyyun siyasa guda biyu waɗanda aka yiwa sakatariyoyi a dukkan jahohi da ƙanan hukumomin Najeriya na lokacin; gine-ginen da aka riƙa maida wasunsu makarantu, asibitoci, da sauran ma’aikatun gwamnati a halin yanzu.
 17. Kyautata Dangantakar Najeriya da Ƙasashen Waje: Gwamnatin shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ta inganta dangantakar Najeriya da ƙasashen waje kamar haka:
 • Farfaɗo da dangantaka tsakanin Najeriya da Ingila: A watan Janairun 1986, shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ya gyara dangantakar Najeriya da ƙasar Birtaniya bayan da ta taɓarɓare a lokacin gwamnatin da ta gabace ta.
 • Gwamnatin shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen wanzar da zaman lafiya a wasu daga cikin ƙasashen Afirka ta yamma, ta hanyar amfani da rundunar sojin haɗin-guiwa (ECOMOG), musamman a ƙasashe irin su Laberiya (Liberia).
 • Buɗe Boda: A ranar 28 ga watan Fabarairu na shekarar 1986, an buɗe bodidin Najeriya da gwamnatin da ta gabace ta ta rufe.
 • Shirin Bayar da Tallafin Fasaha (Technical Aid Corp Scheme): Shiri ne da ake tura matasan Najeriya dan bada gdunmawa a wata ƙasa mabuƙaciya a cikin nahiyar Afirka da yankin Karebiya. Tabbas wannan shiri ya samar da guraben ayyukan yi ga ɗimbin ‘yan Najeriya a ƙasashen waje. Ƙarƙashin wannan shirin matasan da suka samu horo a fannonin kimiyya, fasaha, lafiya, shari’a (science, technology, engineering, law, e.t.c) da sauranu, su ake turawa waɗannan ƙasashe mabuƙata dan bayar da gudunmawa ta tsawon shekaru biyu.

Barinsa Kujerar Shugabancin Najeriya

Bayan soke zaɓen ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993 da gwamnatin shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ta yi, abubuwa sun cukurkuɗe ta yadda har sai da ta kai shi barin wannan kujera ta shugabancin Najeriya a ranar 27 ga watan Agusta na shekarar 1993, inda ya miƙa mulki a hannun gwamnatin riƙon ƙwarya.

Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ya jagoranci Najeriya tsawon shekaru 8 cif-cif, inda ya hau a ranar 27 ga watan Agusta na 1985, ya kuma sauka a ranar 27 ga watan Agusta na shekarar 1993, shekaru 8 ke nan cif-cif, ba daɗi ba ragi.

Siyarsa

Babangida da Abdussalam Abubakar da Goodluck Jonathan

Sannan kuma ya sake yunƙurin tsayawa takarar a shekarar 2011, inda ya fara da ƙaddamar da shafin Intanet domin kamfen ɗinsa. Shima daga baya ya janye saboda ƙoƙarin raɓa aukuwar fashewar bom a Abuja da ake yi da shi.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan