Ɗaya daga cikin matasan da suka ba ƴan uwansu matasa kyakkyawan wakilci

  12

  Matasa suna matuƙar alfahari da irin kyakkyawan wakilci da jagoranci da suke samu daga wajen mai ba shugaban ƙasa shawara a ɓangaren ababen more rayuwa, wato Engr. Ahmad Rufa’i Zakari (San-Turakin Kazaure), saboda duniya ta shaida irin namijin ƙoƙarin da yake yi, da kuma yanda yake yin aikin tukuru ba dare ba rana don ganin bai ba ƴan’uwansa matasa kunya ba.

  Engr. Ahmad Rufa’i Zakari yana ɗaya daga cikin matasa waɗanda Shugaba Muhammad Buhari ya zaɓo daga Jihar Jigawa a shekarar 2019 domin tayashi sauke nauyin al’ummar wannan ƙasa tamu Najeriya, wanda a lokacin shekarunsa 36 a duniya, an zaɓe shi ne bisa tunani da kuma kyakkyawan sa rai akansa cewa zai bayar da gagarumar gudummawar sa wajen ciyar da Najeriya gaba, wanda cikin ikon Allah (S.W.T) sai gashi a shekaru biyu da yayi a matsayin mai ba shugaban ƙasa shawara a ɓangaren ayyuka na musamman kwalliya ta biya kuɗin sabulu, saboda ya gudanar da aikin sa yanda dace, wanda har ya zama abin alfahari ga ƴan’uwansa matasa da ke faɗin Najeriya.

  Engr. Ahmad Rufa’i Zakari yana ɗaya daga cikin mutane waɗanda suka yi nasara tare da samun dacewa, musamman a tsari irin na siyasa, badon komai ba sai don kasancewar sa cikakken haziƙi, fasihi, masanin aiki, cikakken ɗan kishin ƙasa, wanda yake fafutukar samarwa da al’umma kyakykyawar rayuwa wacce tayi daidai da zamani. Ya kuma nunawa ƴan’uwansa matasa cewa tabbas makomar su tana hannun su, amma sai idan sun yarda makomar suke nema, ya nuna musu cewa sune zasu samarwa da kansu kyakykyawar makoma, ta hanyar yin aiki tuƙuru, musamman a lokaci da suka samu wata dama wacce zasu iya yin amfani da ita har su nunawa duniya cewa zasu iya yin duk wani abu da ya shafi wakilci, jagoranci ko kuma shugabanci, kamar yanda shi a yanzu ya kafawa kansa tarihi mai kyau ta hanyar yin amfani da damarsa wajen nunawa duniya cewa idan har za’a ringa ba matasa ire-iren sa dama, to duk wani cigaba da ake tsammani za’a same shi.

  Wannan dama da matashi Engr. Rufa’i ya samu yayi amfani da ita wajen samar da ayyuka na musamman a ɓangaren daban-daban, wanda ya ƙunshi samar da lantarki mai amfani da hasken rana a ƙauyuka da karkara, da kuma wasu daga cikin asibitocin da ke ƙananan hukumomi musamman a faɗin jihar jigawa, ya samarwa da matasa ayyukan yi a ɓangare daban-daban, ya tallafawa rayuwar matasa ta hanyar basu jari domin yin sana’o’i na dogaro da kai, ya kuma tallafawa iyaye mata da sauran ƴammata da jari domin yin sana’o’i na dogaro da kai. Hakazalika yayi nisa sosai wajen taimakon marassa karfi a ɓangaren jinya ko ƙunci na rayuwa, sannan yayi nisa sosai wajen taimakawa ƴan’uwansa matasa a ɓangaren da ya shafi cigaban rayuwar su wanda ya ƙunshi taimaka musu a ɓangaren karatu domin samun ingantaccen ilimi.

  Engr. Ahmad Rufa’i Zakari, ya kasance jarumi mai ƙokarin ganin ya yaƙi duk wata matsala ko ƙalubale, musamman akan abinda ya shafi aikin sa, domin tsamowa al’umma kitse daga cikin wuta, ya kan bi hanya mafi sauƙi tare da yin aiki tuƙuru domin ganin rayuwar al’ummar sa ta inganta, wanda hakan ne yake ba ƴan’uwansa matasa ƙwarin gwiwa akansa domin sun san ba zai taɓa basu kunya ba.

  Abu ne a bayyane idan muka duba za muga cewa tun daga lokacin da aka fara mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999 har zuwa yau, tsofaffin jinin nan dai su ake ta ba dama, ba’a fiye ba matasa manyan damarmarki ba, musamman ma a matakin gwamnatin tarayya, saboda ana tunanin kamar ba zasu iya gudanar da ayyukan da suka dace ba, to amma kyakkyawan wakilci da matasan suka samu daga ƴan’uwansu matasa ire-iren su Engr. Ahmad Rufa’i shi zai ƙara tabbatarwa da duniya cewa matasa zasu iya, wanda hakan ne yasa matasan Jihar Jigawa tun a yanzu suke yin kira da kuma roƙo ga mai girma Gwamna Alh. Muhammad Badaru Abubakar Talamiz da ya ba matasa dama domin su gaje shi a zaɓe mai zuwa na 2023, kamar yanda ya fara basu dama tun a zaɓen ƙananan hukumomi, wanda ƙashi 75% na ƙananan hukumomin Jihar Jigawa matasa ne suke jan ragamar shugabancin su.

  Matasa ya zama dole mu haɗa kai muyi aiki tare, mu manta da banbancin dake tsakanin mu na siyasa, mu sani cewa lokaci ya wuce da za’a dinga amfani damu akai ga nasara amma bayan nasarar ta samu a wofantar danu, karmu manta duk abinda waɗannan tsofaffi suka zama ta dalilin siyasa to muma zamu iya zama, amma dole sai idan zuciyar mu ta yarda da hakan, domin suma wanɗanda muke tayar da jijiyar wuya akansu, ba karfinsu ne ya basu ba, ƙuri’ar muce mu matasa ta basu wannan dama, to saboda me zamu sayar da ƴancin mu dan ƴancin wani? Saboda me zamu gina rayuwar wani mu kuma mu rusa tamu rayuwar?

  A ƙarshe ina kira a garemu da cewar, mu farka daga dogon baccin da nukeyi, mu ɗaura ɗamarar samarwa da kanmu ingantanciyar rayuwa, ta hanyar marawa ƴan’uwanmu matasa baya domin jagorantar akalar shugabancin mu.

  Mutane irin su San-Turaki ba abinda sukafi buƙata adaidai wannan lokaci sai addu’a tare da fatan alkhairi a garesu, Allah (S.W.T) ya cigaba da basu ikon aiwatar da duk wani abu da ya dace ga al’umma.

  Amin.

  Adamu Ɗan Almajiri ya rubuto daga Kazaure a jihar Jigawa

  Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

  Facebook
  YouTube
  Instagram
  Telegram
  Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

  Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan