Fitila: Manyan Rahotonni Da Sharhinsu A Makon Jiya

271
Sheikh Ahmed Gumi

A wannan makon an samu labaru masu dadi musamman game da harkar tsaro a yankunan Arewa masu Gabas, inda a makon da ya gabata muka kawo muku cewa gwamnatin tarayya tare da wasu gwamnonin yankin Arewa sun dauki wasu matakai domin shawo kan har kar tsaro da takici kaki cinyewa a yanki.

A wancan makon mun labarta muku cewa cikin matakan da gwamnonin suka dauka sun hada da: hana cin kasuwannin mako-mako, hana sayar da man fetur a kan tituna da kuma a cikin jarkoki, ka’idance adadin man fetur din da mutum daya zai iya saya wanda bai wuce na naira dubu goma ba, da dai sauran wasu sharruda. Duk da dai da yawa daga cikin dokokin ba suyi wa al’umma wadannan yankuna dadi ba, amma tabbas daga rahotannin da suke fitowa daga wadannan yankuna ana samun nasara akan yaki da wadannan yan ta’adda.

Ku duba: Fitila: Tankade Da Rairayar Rahotannin Yan Jarida A Makon Jiya

Sojoji suna sintiri

Sai dai abinda masu fashin baki da masana harkokin tsaro suke ganin baiken gwabnati akai sune, wasu suna ganin kamata yayi a ce lugudan wutar da sojojin kasar suke yiwa yan ta’addan bawai a wuri daya kawai ya kamata a ringa yi ba, kamata yayi ace duk wuraren nan da ake wadannan ta’addancin an hada da su kamar jahohin Kaduna, Niger, da Kebbi wadanda suke makwabtaka da juna kuma ake samun wadannan tashe-tashen hankula.

Sannan masana dai suna ganin Jiha kamar Kano ya kamata ta dauki wani mataki na musamman, na shirin ko ta kwana, sannan jami’an tsaro a wannan jiha su tsaurara tsaro tare da tattara bayanan shirri don gudan kwararowar wadannan yan ta’adda da ake yiwa lugudan wuta a wadancan yankuna.

Wannan batu na tsaro a wannan mako zamu rufe shi da maganar da malamim nan na Kaduna wato Sheik Ahmed Gumi yayi, a cewar malamin yana ganin bai kamata a ringa yakar yan fashin dajin da makamai ba harma ana karkashe su, shi a ganinsa kamata yayi a yi sulhu da su sannan a basu mafaka makar yadda aka yiwa tsagerun Niger Delta a lokacin marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua.

To amma abinda wannan malami ya kasa ganewa game da wadannan mutane shi ne duk da yana shiga cikinsu yana samo labarai, wadannan mutane ko a baya ansha zama ana yarjejjeniya da su amma suna komawa kan harka tasu.

Sannan wadanan mutane suna da banbanci da tsagerun Niger Delta ta yadda suke gudanar da aiyukansu, dominsu tsagerun Niger Delta basa kashe al’ummuminsu haka kawai kuma basa garkuwa da mutane gama gari.

Wasu labarai kuma masu daukar hankali a wannan sati sun hada da labarun da jaridar Peoples Gazette ta fitar akan tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a Jam’iyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, a labarin da jaridar ta fitar tayi bayani cewa gabda zaben shugaban kasa wadda ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci kasar Amurka kasar da a baya yan adawa suke cewa tsohon mataimakin shugaban kasar an hana shi shiga saboda wasu laifuffika da suke jibi da cin hanci da rashawa.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

Wannan batu dai an dade ana anfani da shi wajen nakasa takarar tashi, sai ga shi ana dafda zaben Atiku ya ziyarci kasar Amurkan.

Sai dai wannna labari da Jaridar ta fitar na nuni da cewa Atiku ya samu damar shiga kasar ne bayan ya biya wasu kudade da suka kai dala miliyan 16.5 wanda a chanjin kudin na wannan lokaci ya kai Naira biliyan 8.76.

Wannan labari da jaridar ta fitar ya yamutsa hazo kuma ya saka ayar tambaya da rudani a zukatan al’umma harda magoya bayan tsohon shugaban kasar domin in dai wannan labari ya kasance gaskiya to lalle zargin da ake yiwa tsohon shugaban kasar akan har kar cin hanci da rashawa zai iya tabbata, domin jaridar tace wadannan kudade anyi anfani da su ne wurin samarwa da tsohon mataimakin shugaban kasar hanyar shiga kasar cikin sauki ba tare da wata barazana ko tuhuma daga mahukuntan kasar Amurka ba.

Harma jaridar ta fitar da sunayen wadanda suka taimaka aka samun damar shiga kasar, wadanda jigogi ne a gwamnatin shugaban kasar Amurka na waccan lokaci wato Donald Trump. Wannan labari ma nan zamu jingine shi, zamu jira muji mai da martanin tsohon mataimakin shugaban kasar kan wannan batu.

A dai makon da muka yi ban kwana da shi ne shugaban kasa Shugaba Muhammadu Buhari ya kai wata ziyarar bude aiyuka a jihar Imo, jihar da tayi kaurin suna game da aiyukan yan tada kayar baya na IPOB masu rajin kafa kasar Biafra.

Tun kafin zuwan nasa dai gwamnan jihar wato Hope Uzodinma ya umarci yan jihar da su zamo mutane masu da’a, sannan kar suyi wani abin Allah wadai akan zuwan shugaban kasar. Sai dai itama kungiyar ta IPOB ta bayar da umarnin hana al’umma fitowa domin tarar shugaban kasar.

A labarun da suke fitowa daga wannan jiha suna nuni da cewa shugaban ya shiga jihar lafiya kuma ya fito ba tare da wani hargitsi ko tarzoma ba. Amma wannan baya hana nasaba da rashin fitowar al’ummar garin domin tarbar shugaban kamar yadda aka saba a wasu jahohin.

A hakikanin gaskiya zamu iya cewa wadannan yan tada kayar baya na IPOB sun yi wani karfi da yake nema ya gagari Kundila, domin ko a baya mun san yadda suke bayar da umarnin kar al’umma su fito suyi harkokinsu kuma hakan yake tabbata, sannan gwabnati bata daukar wani mataki akai, sai kuma gashi zuwan shugaban ma sun aikata hakan.

To wai shin mai hakan yake nunawa?

Da farko dai zamu fahimci cewa gwamnati tana nema ta gaza wurin kare al’ummarta da basu kariya domin su gudanar da uzurunsu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya ba su dama. Sai wani gagarumin abu da yake tasowa a wannan kasa tamu wanda yake nema ya canja fasalin yadda ake raba arzikin kasa da sauran abubuwa.

Wannan abu dai ba wani abu ne ba illa kokarin jihar Lagos da ta Rivers da suke yi domin sauya fasalin yadda ake karbar harajin kayan masarufi da na kanfanunuwa wadda aka fi sani da VAT.

Wadannan jahohi dai tuni sukayi dakoki da suke nuni da cewa su zasu rinka karbar harajin kayayyaki masarufi da kanfanunuwa a jahohinsu, harajin da hukumar karbar haraji ta kasa ce wato FIRS take karbarsa. To amma dai kotun daukaka kara ta dakatarda wadannan jahohi har sai ta saurari karar da hukumar ta FIRS ta shigar a gabanta zuwa ranar 26 ga wannan wata da muke ciki.

To ko ma me wannan kokari na wadannan jahohi yake nufi sannan yake nunawa?

Jaridar DailyTrust ta fitar da wata kididdiga da ke cewa akalla jahohhi 30 zasu shiga tsaka mai wuya na tattalin arziki in har hakan ta tabbata, duba da jahohin ba sa tabuka komai ta hanyar inganta tattalin arzikin jahohinsu sai sauraron dan abinda gwamnatin tarayya take aiko musu duk wata a matsayin kasonsu.

Nasan cewa wannan labari ba zai yiwa al’umma wadannan jahohi dadi ba, musamman yan siyasar jahohin wadanda suka mai da dan kason da ake aikowa abun rabawa a tsakaninsu.

Sai dai masu hankali da sanin ya kamata sun dade suna bawa masu rike da madafun iko a wannan yanki na Arewa sharawa akan yadda zasu inganta harkar tattalin arzikin jahohin amma suka yi burus da wadannan shawarwari ganin cewa gwabnatin tarayya tana basu wani kaso da zasu yi albashi da sauran harkokin gabansu.

Wannan rashin hangen nesa na shuwagabanninmu da tun shekaru masu yawa da suka shude shi ne yake haifar mana da cima baya a wannan yanki namu na Arewa, kuma matukar gwamnatin tarayya zata cigaba da turo wadannan kudade to la budda haka zamu cigaba da zaman dirshan, da jiran tsammni mu da cigaba sai dai mugani a wasu wurare.

Ali Sabo Dan Jarida Mai Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Za a iya samunsa ta aliyuncee@gmail.com

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan