Kwanaki ɗari (100) da rufe shafin Tuwita

141

A ranar 4 ga watan Yunin shekarar 2021 ne shafin Tuwita ya daina aiki a Najeriya bayan da gwamnatin tarayya ta dakatar da shafin sakamakon takun saka tsakanin gwamnatin Najeriya da katafaren kamfanin na ƙasar Amirka.

Tun da farko ma’aikatar yada labarai da al’adu ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa Minista Lai Mohammed ne ya ba da sanarwar rufe shafin na Twitter.

Sanarwar ta ce Minista Lai Mohammed ya ce ana amfani da shafin wajen raba kawunan ƴan ƙasar.

Matakin rufe shafin na Tuwita na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da shafin Tuwita ya goge wani saƙo cikin jerin saƙwannin da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa yana gargaɗin ƴan awaren IPOB.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan