Shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, Alhaji Ado Tambai Ƙwa ya yi Allah wadai da kalaman da tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Muaz Magaji ya ke yi a shafinsa na facebook da sauran kafafen sadarwa na zamani.
Alhaji Ado Tambai Ƙwa ya yi wannan kalamin ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa a kafafen yaɗa sadarwa na zamani Abdallah Ishaq Bataye, ya fitar a yau Litinin.
Sanarwar ta ce yadda Injiniya Muaz Magaji ya ke kalaman shaguɓe ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da sauran mukarabban gwamnatin Kano da shugabancin jam’iyyar APC abin takaici ne kwarai da gaske.

“A madadin mai girma shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Ƙwa muna Allah wadai da irin kalaman da Injiniya Muaz Magaji ɗan Sarauniya ya ke yi akan dukkan jami’an gwamnatin Kano tun daga kan ire-iren shaguɓe da ya ke yi ga gwamna zuwa munanan kalaman da ya ke yi ga dukkan jami’an gwamnatin jihar Kano”
Hakazalika sanarwar ta ƙara da cewa “Ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ƙaramar hukuma ce ta Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kuma dukkan irin cigaban da ake da buƙata ya kawo shi. A Dan haka dukkan mutum mai kishi kuma mai son cigaban wannan karamar hukuma da ma jihar Kano ba ki ɗaya to babu abin da ya da ce sama da godewa Baba Ganduje”
Ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ita ce mahaifar gwamna Abdullahi Umar Ganduje kuma nan ce mahaifiyar Injiniya Muaz Magaji. Kuma Mu’azun ya yi fice wajen sukar ƙunshin shugabancin jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Abbas da kuma sukar kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo.
Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a
Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com
Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp