Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zama gwarzon siyasar Najeriya na shekarar 2019

2372

Mujallar Thinkers da ke birnin tarayya Abuja ta karrama tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da lambar yabo ta babban ɗan siyasa a Najeriya.

Lambar Yabo da Mujallar Thinkers ta baiwa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Tun da farko mai taimakawa tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ne akan harkokin sadarwa, Saifullahi Hassan ne ya wallafa sanarawar karramawar a shafinsa na facebook.

“Mai Girma Jagora Sanata Rabiu Musa, wanda Hon. Mohammed Jamu ya wakilta ya karbi lambar yabo a matsayin “babban ɗan siyasa a ƙasa a shekarar 2019″. Wanda Jarida Thinkers Magazine ta bayar. An yi taron a yau (20th September, 2021) a Sheraton Hotel dake Abuja”

Hon. Muhammad Jamu da wakilci Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a wajen karɓar lambar

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso dai ya mulkin jihar Kano daga shekarar 1999 zuwa 2003, sai kuma ya sake dawowa a shekarar 2011 zuwa shekarar 2015. Haka kuma ya taɓa rike muƙamin ministan tsoron Najeriya.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan