Yau take ranar zaman lafiya ta duniya

353

Ranar 2 ga watan Oktoba ce ranar zaman lafiya ta duniya, wacce Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk shekara, domin jaddada bukatar samun kwanciyar hankali da gudun rikice-rikice.

Haka kuma ranar na nunawa jama’a fa’idar da kwanciyar hankali da fahimtar juna kan haifar.

Makasudin ware wannan Rana dai shine domin a tunatarwa al’umma mahimmancin Zaman Lafiya tare da kuma kawo karshen fadace fadace a tsakanin Jama’a daban daban.

Kama dai daga kan Najeriya zuwa wasu kasashen gabas ta tsakiya har ma da tarayyar Turai da kasashen Amurka, rikici walau na ta’addanci ko kuma yanki na ci gaba da kawo cikas a kokarin da hukumomi da gwamnatoci ke yi na wanzar da zaman lafiya a kasashen duniya daban daban.

A Najeriya dai rikicin Boko Haram a yankin arewaci maso gabas da kuma hare – haren ƴan fashin daji a yankunan arewa maso yamma da ta tsakiya da kuma rikicin kabilanci da addini a jihohin Filato da Kaduna da kuma Benue, da kuma rikicin ƴan awaren IPOB masu rajin kafa ƙasar Biafara a shiyyar kudu maso gabas su ne su ka zamewa Najeriya ƙarfen kafa wajen zaman lafiya da kuma ci gaban al’umma.

Wasu ƴan gudun hijira a Najeriya

Wannan rikici da tashin hankali ya raba mIliyoyin al’umma da gidajensu tare da wanzar da dubban ƴan gudun hijira a sansanoni daban daban.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan