A wannan makon ne shugaban kasa Muhammad Buhari yake halattar taron kasashen duniya na 76 wadda majalisar ɗinkin duniya wato United Nation take shiryawa a duk shekara a birnin New York na kasar Amurka.
Babban abin da yake ɗaukar hankalin yan Najeriya game da halattar wannan taro shi ne wani bayani da aka jiyo mai bawa shugaban ƙasa shawara a fannin yAɗa labarai wato Femi Adesina yana faɗa a tashar talabijin ta Channels inda yake cewa shugaban zai yi bayani ga sauran shuwagabannin ƙasashen duniya kan yadda zasu koyi yadda ake inganta tattalin arzikin ƙasa musamman a lokacin mashassharar tattalin arziki wadda cutar korona ta haifar.
Wannna batu dai yasa masana a bangaren tattalin arziki a Najeriya na jefa ayar tambaya kan wacce shawara ce da shi shugaban ƙasar zai bayar.

Wannan tambayoyi dai ba sa rasa nasaba da yadda ake ganin tattalin arzikin Najeriya ya tababbare, tababbarewar da a ƴan shekarun nan ba a taba ganin irinsa ba. In muka yi duba da yadda hauhawan farashi kaya kullum take ƙaruwa, domin alkaluma sun nuna cewa hauhawar tana ƙaruwa fiye da kaso 100.
Kaɗan daga cikin abubuwan da masana suke bada misali da su sun haɗar da kayan masarufi na yau da kullun, da Gas ɗin garki wadda a kwana-kwanan ya ƙara kuɗinsa da kaso fiye da 100, sai kuma yadda darajar kudin ƙasar a kullum yake ƙara karyewa in aka kwatantashi da dalar Amurka.
A wannan batu na tababbarewar Naira ma ko baya-bayan nan mun ji yadda masana suke bada shawara kan shugaban daya sallami shugaban babban bankin kasar tare da duk masu bashi shawara kan harkar tattalin arziki.
To ko shin duba da wadannan misalai shugaban yana da wata shawarar da ya kamata ya bawa sauran ƙasashe game da wannan? Mai karatu ne zaiyiwa kansa alkalanci.
Sai kuma abu na biyu wanda shi ma ya ɗauki hankalin al’umma wanda ya ke fitowa daga fadar shugaban kasar, shi ma dai wannan batu an jiyo shi ne daga bakin mai bawa shugaban kasa shawara ne akan harkoki yada labarai wato Femi Adesina inda yake cewa ba burin wannnan gwamnati ba ne ta tozarta waɗanda suke ɗaukar nauyin ta’addanci a ƙasar nan a lokacin da aka yi masa tambaya game da bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addancin wanda yayi tsamari a yankin Arewa Masu Yamma.
Wannan batu ma dai ya ɗugunzuma al’umma inda suke ganin baiken gwamnati akan wannan mataki da ta ɗauka. Wasu ma dai suna ganin kawai wasa ne akeyi da hankalin al’ummar wannan ƙasa kan harkokin tsaro ganin yadda yaƙi ci yaƙi cinyewa.
A cewar ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnati wato Abubakar Malami, (SAN) gwamnatin tasu tafi mai da hankali wurin hukunta masu ɗaukar nauyin ta’addanci fiye da tozarta ta su.
Sai dai mai karatu zai yi tambaya kan, shin ta yaya za’a hukunta su ba tare da faɗar ko su waye ba?
A wata hira da gidan Radiyon Arewa tayi da shugaban cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma wato CITAD, Malam Yunusa Zakari Ya’u akan wannan batu, shugaban yace “ko dai subul da baka mai bawa shugaban ƙasar yayi, ko kuma bai san mai yake yi ba”.

Sannan ya kara da cewa in ba burin gwamnati ne ta tozarta waɗannan mutane ba, to burin tane kenan ta ga ana kashe al’umma kenan, domin babu yadda za’ayi ayi hukuncin irin waɗannan mutane ba tare da an baiyana su ba.
A jihar Kano kuma, rikici yana neman ɓarkewa game da shugabancin jam’iyar APC wadda za’ayi zaɓen shuwagabannin jam’iyar na jihar nan ba da deɗewa ba. Rahotannin dake fitowa daga majiya mai tushe a gidan gwamnatin wanda wannan jarida ta rawaito a makon da ya gabata na nuni da cewa gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje na dabda sauya shugaban jam’iyar na riko, Abdullahi Abbas da Muntari Ishaq Yakasai wanda shi ne Kwamishinan aiyuka na musamman. Kuna iya karanta cikakken labarin ta nan Shugabancin APC A Kano: Ganduje na shirin canza Abdullahi Abbas da Mukhtar Ishaq Yakasai
Jam’iyar ta APC a jihar Kano dai tuntuni da ma tana cikin ruɗani da rikice-rikice. Waɗannan rikice-rikice dai sun haɗa da samar da wasu tsaguna a jam’iyar kamar tsagin Barau I. Jibrin wanda sanata ne mai wakiltar Kano ta Kudu, da kuma tsagin dan majalisar mai wakiltar ƙaramar hukumar birni a gwamnatin tarayya wato Sha’aban Ibrahim Sharada wanda sun daɗe suna takun saƙa da gwamnan jahar.
Sai kuma wata rigima ta kwanan nan wadda ta haifu bayan wasu kalamai da mai ɗakin gwamnan, Hajiya Hafsat Umar Ganduje ta furta na fitar da ɗan takarar gwamna a jihar.
A baya da an san tafiyar mataimakin gwamnan jihar wato Nasiru Yusuf Gawuna, da kwamishinan ƙananan hukumomi wato Murtala Sule Garo da kuma shugaban jam’iyar na riko wato Abdullahi Abbas a haɗe take, amma bayan kalaman na mai ɗakin gwamnan sai aka ga sun ware mataimakin gwamnan a tafiyar tasu.
To shi kansa wannan batu, babban al’amari ne da ka iya kawowa jam’iyar targaɗo in an zo zabe.
Wannan batu ma dai na rikicin jam’iyar APC nan zamu barshi duk da jam’iyar ta ɗage zaɓen da ta shirya zata yi na jahohi wanda shi ma masana ke ganin yana da alaƙa da rikicin cikin gidan jam’iyar a wannan mako.
Zamu rufe wannan shafi namu na wannan mako ne da batun ɗumamar yanayi wanda ya tasarwa duniya.
Ko a baya kun karanta a wannan shafi inda muka baku labarin yadda ambaliyar ruwa ke barazana da rayukan al’ummar duniya musamman a kasshe irinsu Indiya, China, Jamus, Najeriya da dai sauran su.
A wannan mako babban abinda ke ɗaukar hankalin duniya shi ne gobarar daji wacce ta tasarwa ƙasashe irinsu Australia, Amurka da kasar Spain.
Rahotanni dake fitowa daga ƙasar Spain na nuni da cewa yanki tsuburin La Palma na ƙasar ya shiga wani mawuyacin yanayi inda yayi sanadiyar kwashe mutane fiye da 8000 a kauyuka 6.
Ko a wannan taron da ake gabatarwa na majalisar ɗinkin duniya na wannan shekara, shugaban ƙungiyar Antonio Guterres yayi kira ga ƙasashe masu karfin tattalin arziki da su kara ƙaimi wajen magance ɗumamar yanayi a duniya.
Kiranmu a wannan shafi shi ne kowa daga cikin al’umma yana da gudunmawar da zai iya bayarwa domin mu gudu tare mu tsira tare.
A matsayinmu na ɗai-ɗaikun al’umma zamu iya bayar da tamu gudunwar ta hanyar inganta muhallinmu kamar shuka bishiyu, da gujewa sare su da kuma gyara mugudannan ruwa don kaucewa ambaliyar ruwa.
Ali Sabo Dan Jarida Mai Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Za a iya samunsa ta aliyuncee@gmail.com
Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a
Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com
Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp