Allah ne ya Ƙaddara Zama na Sarki ba don na fi Kowa ba – Sarkin Gaya

191

Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya karɓi shaidar kama Aiki a Matsayin Sabon Sarkin Gaya.

A yammacin yau Litinin, Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya miƙa takarda shaidar kama aikin ga Sabon Sarkin wanda aka sanar da zaɓensa cikin daren Lahadin nan data gabata.

A yammacin yau Litinin, Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya miƙa takarda shaidar kama aikin ga Sabon Sarkin wanda aka sanar da zaɓensa cikin daren Lahadin nan data gabata.

Hakan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan rasuwar Mahaifinsa Alhaji Ibrahim Abdulƙadir, a cikin makon da ya gabata. Da yake gabatar da Jawabin sa Sarkin Gaya Alhaji Aliyu ya bayyana wasu kalamai dake Tabbatar da neman haɗin kan Al’ummar masarautar baki ɗaya. Ku Karanta: Tsakanin hukumar tace fina-finai, Afakalla, Majalisar dokokin Kano da ƴan Kannywood

“Allah ya ƙaddara na zama Sarkin Gaya badon nafi kowa ba, haka Kuma Ina fatan ‘yan uwana da su ka nemi sarauta za su zo mu haɗa kanmu wajen ciyar da Masarautar Gaba”.

Sarkin Gaya na Karɓar Shaidar Kama Aiki Tare da Gwamna Ganduje

Taron dai ya gudana a babban ɗakin taro na fadar gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje.Ya zuwa yanzu dai ƙasar Gaya ta Fara daukar harami cikin murna da sabon Sarkin Gaya Wanda ya karɓi shaidar kama aiki a yau Litinin.

Ya zuwa yanzu dai ƙasar Gaya ta Fara daukar harami cikin murna da sabon Sarkin Gaya Wanda ya karɓi shaidar kama aiki a yau Litinin.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram


Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum  WhatsApp

Turawa Abokai

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan