Sarkin Kano Aminu Ado Ya Zama Uban Jami’a

403

An naɗa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin uban jami’a mai zaman kanta ta Al-Istiqama dake ƙaramar hukumar Sumaila a jihar Kano.

Shugaban Jami’ar Honorabul Abdulrahman Kawu Sumaila, ne ya gabatar da takardar naɗin ga Mai Martaba Sarkin Kano a ranar Laraba 29 ga Satumba, 2021.

Da yake miƙa takardar ga Mai Martaba sarkin Kawu Sumaila ya ce sun yi la’akari da kwarewa da gogewa da Sarkin ya ke dasu tare da ƙoƙarin da ya ke yi wajen inganta harkokin Ilimi a jihar Kano da Ƙasa baki ɗaya.

A Jawabinsa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna farin Cikinsa tare da bada tabbacin Zai yi duk mai yiwuwa wajen ci gaban Jami’ar dama Ilimi baki ɗaya.

Kawu Sumaila da Sarkin Kano

Mai martaba sarkin ya buƙaci mawadata dake cikin al’umma da su mai da hankali wajen bada tasu Gudunmawar don ci-gaba Ilimi a Kano da ƙasa baki ɗaya.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan