Shugabannin da suka mulki ƙasar nan tun bayan samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa ya kasance Prime Minista na farko a ƙasar nan tun a jamhuriya ta farko.
Yayi rayuwarsa tsakanin shekara ta 1912 zuwa 1966. An haifeshi a garin Tafawa Ɓalewa dake jihar Bauchi. Yayi karatun sa a Makarantar Koyon Malanta dake Katsina tsakanin 1928 zuwa 1933.
Bayan rasuwar sa ta sanadiyyar juyin mulkin da akai musu hakan ya kawo mulkin Manjo Janar Johnson Thomas Aguiyi-Ironsi, Shugaban Gwamnatin Sojan kasarnan na farko . An haife shi ranar 3 ga Maris, 1924 a garin Umuahia-Ibeku dake jihar Abia, inda ya kwashe kwanaki 194 akan karagar mulki.
Bayan hambarar da gwamnatin Ironsi da wasu daga cikin sojoji su ka yi sai Janar Yakubu Gowon, yahau mulkin ƙasa, Yakubu Gawon dai an haife shi a ranar 19 ga Oktoba, 1934. Ya fito daga ƙabilan Angas dake Jihar Filato. Iyayensa sunyi ƙaura zuwa Wusasa dake Zaria a Jihar Kaduna, domin yaɗa addinin Kirista, bayan kifar da gwamnatinsa Janar Murtala Ramat Muhammad, ya haye karagar mulkin ƙasa.

Janar Murtala Ramat Mohammed An haifeshi ranar 8 ga Nuwamba, 1938. Ya rasu ranar 13 Fabrairu, 1976.
Janar Murtala Mohammed ya zama Shugaban ƙasar nan na sojane bayan kifar da Gwamnatin Yakubu Gowon, da yaje ƙasar Addis Ababa dan halartan taron ƙungiyar ƙasashen Afrika.
A ranar 13 ga wata Fabrairu, 1976 aka hallaka Murtala Mohammed, a wani yunƙurin kifar da gwamnatin soja dake ƙarƙashin sa.
Hakan ya kawo Olusegun Obasanjo, wanda aka haifeshi ranar 5, Maris,1937 a garin Abeokuta na jihar Ogun. Yayi Shugabancin kasar a matsayi Sojan tsakanin 13 Fabrairu 1976 zuwa 1 ga Oktoba, 1979. Inda ya miƙa mulki ga gwamnatin farar hula, ƙarƙashin Alhaji Shehu Shagari
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya maye gurbin Shehu Shagari inda Gwamnatinsa tazo da zafi inda ta ƙaddamar da yaƙi da cin hanci da rashawa.
Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wanda akewa lakabi da IBB shi ne wanda yakawo karshen mulkin shugaba buhari sanadiyyar wani juyin mulkin soji da’aka gudanar andai haifeshi ranar 17 ga watan Agusta, 1941.Ya mulki Nijeriya, daga 27 ga Agusta 1985 zuwa 27 ga Agusta, 1993. Ya tsallake rijiya da baya sau da yawa a lokacin da yake mulki.
Mulkin Ibrahim Badamasi Babangida yazo ƙarshene bayan barin kujeran mulki da yayi ba shiri inda yanada Chief Earnest Shonekon amatsayin shugaban rikon kwarya, an haifi Shoneken, a ranar 9 ga watan Mayu, 1936 a garin Lagos. yayi koyon aikin Lauya a ƙasar Britaniya.
Rasuwar Marigayi Umar Musa ‘Yar Adu’a ne ta kawo mulkin tsohon shugaba Goodluck Ebele Jonathan wanda aka Haifa 20-nuwamba-1957 wanda kuma ya kasance mataimakine ga marigayi ‘Yar’aduwa inda ya mulki kasarnan na tsawon shekaru 5, bayan zaben shekara ta 2015 ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya dawo a karo na biyu ya samu nasarar ɗarewa mulkin ƙasar nan a ranar 29 ga mayu 2015 wanda har yanzu yake ci gaba da jagorancin kasarnan bayan samun nasara a neman wa’adin mulki na biyu, wanda ayau 1 ga watan October ne kasarnan ke murnar cikarta shekaru 61 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.