Siyasar Kano: Hotunan Muhuyi Magaji Rimin Gado sun cika birnin Kano

604

A jihar Kano, al’ummar garin sun wayi gari da ganin wasu hotuna ko posta ta kamfe na dakataccen shugaban Hukumar Karɓar ƙorafe-ƙorafe da cin hanci da rashawa ta jihar KPCACC, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado.

Hotunan na nuna cewa Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado yana neman takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar APC mai mulkin jihar a shekarar 2023.

Wata ƙungiya ce dai wadda ke kiran kanta da G20 Feru da kuma Musbahu Hussain ne su ka dauki nauyin buga hotunan.

Sai dai wakilin Labarai24 ya tuntubi Musaddiq Kabir Adam, wanda makusanci ne ga Barista Muhuyi ɗin akan wannan batun inda ya bayyana cewa su dai haka su ke ganin hotunan kuma su ke jin labari kamar sauran al’ummar jihar Kano.

Musaddiq Kabir Adam ya ƙara da cewa akwai ƙungiyoyin da su ka tuntubi Muhuyi Magajin akan wannan kiraye – kiraye amma har yanzu bai ce komai ba tukunna.

“To dai gaskiya maganar fasta (Poster) muma labari mu ke samu kuma muma muna gani a gari. Idan na ce maka mutane ba su same shi mai gida akan cewa suna buƙatar sa ya fito takara ganin yadda su ke ganin cewa al’ummar jihar Kano shaidu ne wajen yadda kauna take tsakanin sa da talaka kuma ya ke tsaya mu su akan al’amuran su to wannan na yi ma ƙarya”

Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado

“Mutane daga sassa- sassa daban-daban tare da wasu daga cikin ƙungiyoyi kama daga ƙungiyoyin ƴan kasuwa da na addini da na ɗalibai da sauransu sun tuntuɓe shi tare da nema zama da shi kuma kowanne daga cikinsu na bayyana sha’awar sa akan ganin ya fito neman kujerar gwamnan jihar Kano a shekarar 2023 amma dai shi mai gida har kawo yanzu bai ce komai ba akan wannan batu”

“Dama mutane ne su ke zaɓar shugabanin su to idan suna ganin ya da ce ba za mu hana su ba, sai dai kawai suna buƙatar su ji ta bakin sa” In ji Musaddiq Kabir Adam.

Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado

Barista Muhuyi Magaji dai ɗan siyasa ne kuma ɗan gwagwarmaya mai rajin yaƙi da cin hanci da rashawa a jihar Kano.

Domin ko a lokacin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau tsakanin 2003 zuwa 2011 yayin da Muhuyi yake matsayin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Rimin Gado, ya taɓa kai ƙorafi ga hukumar EFCC ta ƙasa kan wasu kuɗaɗen ƙaramar hukumar da suka maƙale.

Haka kuma al’umma a jihar Kano tare da sauran masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewa Muhuyi ya yi matukar ɗaga darajar hukumar ta cin hanci da rashawa ta jihar, har ta zama hukumar da jami’an gwamnati da attajirai da ƴan kasuwa da sarakai suke tsoronta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan