Katsewar Facebook, WhatsApp da Instagram ta haifar da asarar miliyoyin Daloli

144

A jiya litinin da yamma shafukan sada zumunta na Facebook da WhatsApp da kuma Instagram, su ka samu wata ƴar-tangarɗa, wadda ta sa mutane da dama basu iya shiga shafukan zumuntar, na tsawon wasu awowi.

Masu sharhi akan al’amuran yau da kullum na hasashen cewa matsalar da aka samu a jiya, na iya janyo wa kamfanin asarar da ta kai ta sama da dala miliyan 3, na harajin talluka a iya wannan taki.

Sai dai tuni wanda ya ƙirƙiro Facebook, Mark Zuckerberg, ya nemi gafara ga biliyoyin mutane a fadin duniya sakamakon katsewar shafukansa. WhatsApp, da Instagram da shi kansa Facebook sun daina aiki na awanni shida amma a yanzu sun dawo.

Katsewar dai ta hana mutane biliyan uku da rabi da ke amfani da shafukan damar shiga domin musayar ra’ayi da labarai da kuma sada zumunta.

Lamarin na faruwa ne kwana guda bayan wata mai bankada da ta taba aiki da kamfanin ta fallasa cewa Facebook ya fi fifita ribar da yake hankoron samu fiye da kare masu amfani da shafukansa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan