Jam’iyyun Adawa Na Najeriya Sun Yi Kira Ga Majalisa Ta Tsige Buhari

249

Gamayyar Haɗaɗɗun Jam’iyyun Najeriya, CUPP, ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta fara shirye-shiryen tsige Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Mai Magana da Yawun CUPP, Ikenga Imo Ugochinyere ne ya yi wannan kira ranar Laraba a wani taron manema labarai.

Mista Ugochinyere ya yi zargin cewa Shugaba Buhari ya ci zarafin ofishinsa, ya yi rashin ɗa’a kuma ya gaza kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Ya ce rayuwar ‘yan Najeriya ta yi arha a halin yanzu, yadda shugabanni “ba sa ma nuna tausayi kwata-kwata”.

CUPP ta yi kira ga ‘yan majalisu ‘yan hamayya su yi aiki da masu kishin ƙasa waɗanda ta ce “an danne su a jam’iyyar APC” kuma suke neman mafita su fara shirin tsige Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan da Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ba tare da ɓata lokaci ba.

A cewar CUPP, shugabannin majalisun biyu sun gaza jagorantar abokan aikinsu wajen sa ido akan gwamnatin.

“An daina ma girmam su kwata-kwata saboda da yawan ministoci sukan yi yi shakulatin ɓangaro da su idan sun kira su.

Mista Ugochinyere ya ce CUPP ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayyar inda take roƙon kotu ta umarci Majalisar Dokokin Najeriya ta binciki Shugaba Buhari bisa zarge-zargen da ake yi masa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan