Dole Mu Ciyo Bashi Don Mu Ƙarasa Ɗimbin Ayyukan Da Muka Fara— Buhari

307

Dole Sai Mun Ciyo Bashi Kafin Mu Aiwatar Da Kasafin Kuɗin 2021— Buhari
Ministar Kuɗi, Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Ƙasa, Zainab Ahmed, ta ce Gwamnatin Tarayya za ta aiwatar da giɓin kasafin kuɗin tiriliyan N2.258 ta hanyar cin bashi a cikin gida da waje.

Minista Zainab ta bayyana haka ne ranar Laraba a yayin taron tattaunawa na Majalissar Zartarwa ta Ƙasa, FEC, wanda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a Abuja.

Ministar, wadda ta samue rakiyar Ministan Shari’a kuma Babban Atoni Janar na Ƙasa, AGF, Abubakar Malami da Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ta ce FEC ta amince da kasafin kuɗin baɗi da ya kai tiriliyan N16.39.

Da take bayanin me ya sa Najeriya za ta ciyo bashi duk da suka da take sha, Zainab ta ce za a ciyo bashin ne don kammala manyan ayyukan da gwamnati ta fara, tana mai cewa kuɗaɗen shiga da ake samu ba za su isa a yi ayyukan ba.

“Idan muka dogara da kuɗaɗen shiga da muke samu, kodayake dai kuɗaɗen shigarmu sun ƙaru, ba za a iya gudanar da ayyukan gwamnati ba da suka haɗa da biyan albashi da sauransu.

“Saboda haka muna buƙatar mu ciyo bashi don gina waɗannan ayyuka da za su tabbatar mana da ci gaba mai ɗorewa.

“Ciyo bashi da Najeriya ke yi ya damu mutane ya kuma jawo tattaunawa da yawa, amma idan ka duba yawan kuɗin, yana cikin abubuwa na lafiya kuma taƙaitattu. A July 2021, jimillar bashin da aka ci shi ne kashi 23 cikin ɗari na GDP”, in ji ta.

“Idan ka kwatanta bashinmu da na sauran ƙasashe, mu ne na ƙarshe a wajen cin bashi a yankin, ƙasa sosai idan aka kwatanta da Misra, Afirka Ta Kudu, Brazil da Angola”, ta ƙara da haka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan