Takun Saƙa: Ganduje Ya Hana Joɓe Gudanar Da Ayyuka A Dawakin Tofa

247

Takun saƙar dake tsakanin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado, Tijjani Abdulkadir Jobe na ci gaba da haifar da matsala a jihar Kano, a cewar wani rahoto na musamman da jaridar Intanet, Solacebase ta wallafa.

Jaridar ta ce wannan takun saƙa ta sa Gwamna Ganduje ya hana aikin gina azuzuwa a makarantun firamare da sakandare a yankin.

Injiniya Jobe, a matsayin sa na Shugaban Kwamitin Wakilai Kan Bunƙasa Karkara ya samo ayyuka na biliyoyin naira daga Majalisar Wakilan, ayyukan da za a gudanar a mazaɓar tasa, a cewar rahoton.

Ayyukan da Jobe ya samo sun haɗa da samar da ruwan sha, hanyoyi, wutar lantarki, tallafa wa matasa da kuma ilimi a ƙananan hukumomin uku da yake wakilta.

Sai dai a wani abu da ya yi kama da taɗiya irin ta siyasa, Gwamna Ganduje ya hana aiwatar da waɗannan aikace-aikace sakamakon jan zare da ake yi yi tsakanin sa da Jobe.

Abin da ya jawo wannan rigima shi ne Gwamna Ganduje yana so ya maye gurbin Jobe da ɗansa, Injiniya Umar Abdullahi Ganduje da aka fi sani da Abba zaɓen 2023.

Wasu majiyoyi na kusa da iyalin Gwamna Ganduje sun ce ƙoƙarin tsayar da Injiniya Umar a matsayin ɗan takara ya sa an samu matsala da babban ɗan Gwamnan, Abdul’aziz Abdullahi Ganduje, wanda shi ne ya fara nuna sha’awarsa ta yin takara a mazaɓar ta Dawakin Tofa.

Sai dai Uwargidan Gwamna Ganduje, Farfesa Hafsat ta yi taɗiya ga wannan buƙata, inda ta nuna Abba take so.

Abba ma’aikaci ne a Hukumar Kula da Kamfanonin Sadarwa ta Ƙasa, NCC, kuma ya tafi hutu shekaru biyu da suka wuce, inda ya dawo Kano don ya taimaka wa mahaifinsa tafiyar da gwamnati.

Abdul’aziz Ganduje shi ne wanda ya kai ƙarar mahaifiyarsa, Farfesa Hafsat ga Hukumar Hukunta Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’anati, EFCC bisa wata baɗakalar filaye.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan