Kotu Ta Hana Yahudawa Yin Ibada A Masallacin Ƙudus

407

Wani alƙalin birnin Ƙudus ya tabbatar da dokar ‘yan sanda da ta haramta wa wani Bayahude da aka gani yana ibada a harabar Masallacin Ƙudus.

Alƙalin dai ya yi watsi da hukuncin wata ƙaramar kotu ne wadda ta goyi bayan Bayahuden wanda wasu ke ganin zai haifar da tashin hankali, a cewar BBC Hausa.

Jaridar ‘The Times’ ta Isra’ila da ta ruwaito wannan labarin ta ce hukuncin kotun na ranar Juma’a na zuwa ne bayan Ministan ‘Yan Sanda, Omer Bar-Lev ya ɗaukaka ƙara a ranar Talata da ta gabata inda ya yi gargaɗin cewa hukuncin ƙaramar kotun zai iya haifar da wani mummunan tashin hankali, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

A hukuncin da ya yanke, alƙalin kotun Aryeh Romanov ya tabbatar da haramta wa Yahudawa yin ibada a harabar da aka amince wa Musulmi su yi ibada.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan