Tinubu Ya Dawo Najeriya Bayan An Yi Masa Aiki A Ƙafarsa

164

A ranar Juma’a ne Bola Tinubu, Ministan Ayyuka kuma Jagoran Jam’iyyar APC na Ƙasa, ya dawo Najeriya bayan an yi masa aiki a gwiwarsa, a cewar ofishinsa.

Mr Tinubu, wanda an yi imanin yana da burin yin takarar shugaban ƙasa, ya shafe makonni a ƙasashen waje da suka haɗa da Ingila, inda ya zauna a gidan Gwamnan Jihar Osun, Gboyega Oyetola.

Takardun Fallasa na Pandora Papers sun nuna yadda Mista Oyetola ya sayi wannan gida ta hanyar badaƙala inda ya yi amfani da asusun hamshaƙin ɗan kasuwar nan Kola Aluko.

A yayin da yake zaune a gidan, Mista Tinubu ya karɓi baƙi da dama da suka haɗa da Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila.

“Ya dawo lafiya lau daga aikin gwiwa da aka yi masa, kuma zai ci gaba da yin ƙoƙari wajen bunƙasa mulkin dimokuraɗiyya a ƙasarmu”, in ji ofishinsa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan