Fitila: Sharhi Da Fashin Baƙin Manyan Rahotannin Makon Jiya

225

A wannan makon zamu yi duba ne kan wasu muhimman abubuawa guda uku da suka faru a wannan kasar tamu.

Na farko zamuyi duba akan kasafin kuɗi na shekara mai zuwa wanda shugaba Buhari ya gabatar a zauren majalisa, sannan zamuyi duba akan sabon bincike wanda wasu gungun yan Jarida guda 600 daga ƙasashe 170 suka yi kan yadda shuwagabannin ƙasashe suke sace da ɓoye kuɗin al’ummarsu a ƙasashen ƙetare.

Sai kuma gayyatar da hukumr yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC tayi yiwa mai ɗakin gwamnan jihar Kano, Hajiya Hafsat Umar Ganduje kan zarginta da wata badaƙala wadda ɗanta ya shigar.

A wannan makon ne dai shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar baɗi a gaban majalisa domin neman sahale masa kan kasafin kuɗin kamar yadda doka ta tanada, kasafin da ya kai Naira Tiriyan 16.39.

Mafi yawan kasafin dai kamar yadda alƙalumma suka nuna zai fi mai da hankali ne akan ayyuka na yau da kullum. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, fitar kasafin ke da wuya masana suka fara cece kuce game da yadda kasafin yafi karkata akan harkoki na yau da kullum.

Ana ganin cewa ƙasar nan ta daɗe bata lura da ɓangarorin manya aiyuka waɗanda sune idan aka samar da su zasu samarwa da ƴan ƙasa aiyukan yi sannan su rage zaman banza ga matasa.

Sai kuma yadda gwamnati tayi kasafin da kuɗaɗe masu yawa waɗanda ake ganin duba da tasirin kasafin wannan shekara da muke ciki wanda a turance ake kira da “Budget Performance” tabbas zamu fahimci cewa gwamnati ta ɗebo da zafi, kuma da wahala a samu a aiwatar da shi kamar yadda ya kamata.

Haka zalika idan muka yi duba da yadda za’a samar da kuɗaɗen da za’a aiwatar da kasafin kuɗin, shi ma dai wannan wani babban abu ne da ya kamata al’umma su saka ayar tambaya akansa, domin a cikin bayanin shugaban yace ana sa ran a kowacce rana Najeriya zata ringa fitar da gangar ɗanyen mai miliyan daya da digo bakwai, sannan za’a ciyo bashi na Naira Tiriliyan 6.

Su kansu waɗannan batutuwa abubuwane masu tsoratarwa, waɗanda duk mai hankali cikinsa zai ɗuri ruwa daga jin wannan batu, ga dalili:

A kasafin kuɗi na wannan shekara da shugaba Muhammadu Buhari yayi shi ma dai gwamnatin tayi hasashen cewa zata rinƙa fitar da ɗanyen gangar mai 1.7m amma kamar yadda alƙalumma suka nuna ƙasar bata iya fitar da gangar da ta wuce 1.5m inda ake samu gibi na ganga 200,000 a kowacce rana, wanda shi ma yana da alaƙa da abinda yasa kasafin na bana bai taɓuka abin azo a gani ba, sai zallar alƙawarruka da aka ɗauka aka kasa cikawa.

Sai abu na biyu a wannan ɓangare wanda shi ma masana na ganin abu ne mai kamar yuwa duk da dai a yanzu darajar man ta tashi a kasuwar duniya.

Shugaban yace an ɗora kasafin akan sayar da kowacce gangar mai akan Dalar Amurka $52 wanda shi ma bashi da tabbas ganin yadda kasashe masu cigaba suke rage amfani da man fetur ɗin a ɓangarori da dama.

Sai batu na biyu wanda shi ne maganar cin bashi wanda ya kai Naira Tiriliyan 6.258. Wannan ƙasa dai tun zuwan wannan gwamnati basussukan da ake binta kullum ƙara ƙaruwa suke, sannan abubuwan da ake cewa za’ayi in an ciyo bashin sau da dama ba’ayisu wanda wannan ya saka ƴan ƙasa da dama suke da shakku kan da yawa daga alƙawarruka na wannan gwamnati.

Haka zalika su kansu ƙasashe da hukumomi masu bayar da wannan bashi suna duba abubuwa da dama kafin bayar da bashi ga ƙasashe musamman masu tasowa duba da da yawa daga cikin ƙasashen basa amfani da bashin da aka basu a inda suka yi alƙawarin zasu yi.

To wannan ma dai zai iya kawowa kasafin kuɗin tarnaki domin ƙasashen yamma sun sanya ido akan ƙasar musamman ta yadda ƙasar take kama karya ga ƴan ƙasa da kuma yadda kullum take ƙoƙarin hana yan ƙasar fadar albarkacin bakinsu, wanda har a kwanakin baya ta kai ga ƙasar ta rufe shafin sadarwa na twitter.

Sai batu na biyu da zamu tattauna a wannan mako wanda wata haɗakar yan jaridu na duniya suka fitar da wani bincike da ake kira da Pandora Papers wadda ke dauke da bayanai na yadda manyan shugabannin duniya suke sacewa da ɓoye dukiyar al’ummar ƙasarsu a wasu wurare ba tare da sanin ƴan ƙasar ba.

A Najeriya rahoton na Pandora Papers ya fitar da sunayen wasu manyan yan siyasa da tsofaffin sojoji da kuma yan kasuwa waɗanda suka saci dukiyar ƙasar suka ɓoye a ƙasashe na ƙetare da kuma waɗanda suka ki bayyanawa hukumomin ƙasar tarin dukiyarsu lokacin da suka ɗare mukaman iko kamar yadda dokokin ƙasar suka tanada.

Cikin irin waɗannan mutane da wannan bincike ya biyu ta kansu sun haɗa da tsohon dan takararar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP wato Peter Obi, da tsohon kakakin majalisar dattawa Bukola Saraki, da tsohon ministan mai a ƙasar, Theophilus Danjuma, da Mike Adenuga, da gwamnan Niger Abubakar Sani Bello, da sanata Andy Uba, da Aliko Dangote, Wale Tinubu, da malamin addinin kiristancin nan daya rasu wato T.B Joshua, da tsohon kakakin majaisar dattawa sanata David Mark, waɗannan da ma wasu sauran masu riƙe da madafun iko a ƙasar kamar mai rikon kwarya shugabancin hukumar shige da fice ta ruwa wacce ake kira da NPA wato Bello Kolo.


Sai kuma gwamnan Kebbi na yanzu wato Atiku Bagudu wanda ake zargin makusanci ne ga tsohon shugaban kasa marigayi General Sani Abacha kuma shi ya tallafawa tsohon shugaban wurin fitar a maƙudan kuɗaɗe zuwa kasashen ƙetare.

Waɗannan mutane dai kamar yadda binciken ya bayyana ana zargin da yawa daga cikinsu da cin amanar ƙasa ta hanyar sace dukiyar ƙasar su kai su wasu ƙasashe tare da taimakon waɗansu mutane da kamfanunnuwa da suka kƙware wurin ɓoye kuɗaɗen haram a kasashen ketare.

Ana ittifakin cewa kuɗaɗen da wasu daga cikin waɗannan mutane suka sace ya isa ya fitar da ƙasar nan daga cikin ƙangin da take ciki.

Tuni dai ƙasashe irinsu Kenya da Pakistan suka ɗauki alwashin cewa zasu gudanar da cikakken bancike akan al’amarin kuma duk wanda aka tabbatar da zargin da ake yi masa zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Haka dai ƙasashe irinsu Germany tuni suka fara tsaurara dokoki na wuraren ma’ajiyar kuɗaɗe a kasar.

A ƙarshe binciken yace duk da dai wasu daga cikin waɗannan mutane babu cikakkiyar hujjar cewa satar kuɗin suka yi amma yana fata gwamnatocin ƙasashen da abin ya shafa zasu ɗauki matakai kan batu.

Sai abu na uku wanda da shi ne zamu rufe wannan shafi a wannan mako.

Rahotanni da ke fitowa daga jihar Kano yana nuni da cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta cafke mai ɗakin gwamnan jihar bisa ƙarar da ɗanta Abdulaziz Abdullahi Umar Ganduje ya shigar gabanta kan zargin mahafiiyar tasa da yin ba daidai ba kan cinikin wani fili wanda ya wuce gaba aka yi.

A cewar jaridun ƙasar cikin harda wannan jarida, hukumar ta EFCC tayi awon gaba da mai ɗakin gwamnan bayan aike mata da takardar gayyata wanda bata amsa ba, sai dai bayan wasu yan bincike da tambayoyi an samu labarin sakin mai ɗakin gwamnan kan sharadin cewa zata kawo kanta a duk lokacin da aka neme ta.

Shi ma wannan batu nan zamu bar shi, kuma zamu cigaba da bibiya.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Ali Sabo Dan Jarida Mai Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Za a iya samunsa ta aliyuncee@gmail.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan