An Dakatar Da ‘Yan Majalisa Biyu A Zamfara Bisa Zargin Su Da Talla Wa ‘Yan Ta’adda
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta dakatar da mambobinta sakamakon zargin su dada alaƙa da ‘yan bindiga masu fashi da satar mutane.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da da Jami’in Huɗɗa da Jama’a na Majalisar, Mustapha Jafaru Kaura ya fitar a ranar Talata.
Sanarwar ta ce an dakatar da ‘yan majalisar ne na tsawon wata uku zuwa lokacin da aka kammala bncike kan wannan zargi.
Mustapha ya ce ‘yan majalisar biyu za su gurfana gaban Kwamitin Ɗa’a da na Tsaro waɗanda za su yi bincike a kansu.
‘Yan majalisar da aka dakatar su ne Yusuf Muhammad Anka mai wakiltar ƙaramar hukumar Anka da kuma Tukur Bakura mai wakiltar Bakura.
Sai dai ‘yan majalisar biyu da ake zargi ba su cikin zauren majalisar lokacin da aka zartar da matakin da kuma zargin da ake musu.
“Bita da ƙullin siyasa ce kawai, saboda mun yi yunƙurin tsige kakakin majalisa”, Yusuf Muhammad, ɗaya daga cikin ‘yan majalisar da ake zargi ya shaida wa BBC Hausa haka.
Jihar Zamfara dai ta daɗe tana fama da matsalar tsaro—matsalar da a iya cewa tana ƙoƙarin kassara jihar.