Gana Za Ta Fara Aika Masu Yaɗa Hotunan Batsa A Ƙasar Gidan Yari

305

Gwamnatin Ghana za ta fara hukunta duk wanda ya yaɗa hotuna ko bidiyon batsa musamman na mata da ƙananan yara, ƙarƙashin wata sabuwar doka, a cewar wani rahoto na BBC Hausa.

Dokar na ƙunshe cikin kundin dokar tsaron Intanet ta 2020, kuma za ta yi ƙoƙarin magance matsalar yadda ake yaɗa hotunan mutane na batsa wani lokaci da nufin tozarta wasu.

Babban Jami’in ‘Yan Sanda Mai Kula da Laifukan da Suka Shafi Intanet na Ghana, ACP Dakta Gustav Herbert Yankson ya yi gargaɗi musamman ga mata, su daina tura wa maza hotunansu na batsa ko da kuwa mazajensu ne.

A cewar jami’in, hotunan za su iya faɗawa ga mugun hannu, musamman idan an sace wayar ko kuma an yi kutse.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan