Ni Ne Halattaccen Shugaban APC A Kano— Ɗanzago

447

Ni Halattaccen Shugaban APC Ta Kano— Ɗanzago
Sabon Shugaban tsagin Jam’iyyar APC a Jihar Kano, Ahmadu Haruna Zago, ya ce tsaginsa ne ya gudanar da halattaccen zaɓe da uwar jam’iyyar ta ƙasa ta amince da shi.

Yayin da Ɗanzago ya zama shugaban jam’iyyar APC ta Kano a zaɓen da tsohon Gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ya jagoranta a Janguza, Abdullahi Abbas kuma ma ya zama shugaba a zaɓen da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta.

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar Intanet ta Daily Nigerian ranar Lahadi da daddare, Ɗanzago ya ce zaɓen da Gwamna Ganduje ya jagoranta ba ya kan doka.

“Zaɓenmu shi ne wanda doka da uwar jam’iyyar APC suka amince da shi. Mun cika dukkan sharuɗɗa da ake buƙata. Maganar da jam’iyya take yi shi ne waɗanda suka yi wani zaɓe na daban, ba mu ba.

“Da farko, Abdullahi Abbas bai taɓa biyan haraji ba, kuma bai sauka daga shugabancin riƙo ba kafin gudanar da zaɓe. A takardun da ya miƙa wa uwar ta ƙasa, ba takardar shaidar biyan haraji.

“Na biyu, Farfesa Mohammed Sani Bello ne ya sanar da sakamakon zaɓenmu, wanda dama shi uwar jam’iyya ta turo. Yanzu, faɗa min sunan mutumin da ya duba zaɓensu.

“Kuma sun yi sulhu a lokacin da sauran ‘yan takara da suke son shiga zaɓe. Amma a ɓangarenmu, kodayake dai Nura Hassan Ungogo da Babanlungu sun janye min, duk da haka sai da aka yi zaɓe”, in ji Ɗanzago.

Sai dai lokacin da Daily Nigerian ta tuntuɓi Abdullahi Abbas, sai ya yi watsi da iƙirarin Ɗanzago, yana mai cewa uwar jam’iyyar APC ba ta san akwai wani tsagi a jihar Kano ba.

Ya ce uwar jam’iyya jagorancin Gwamna Ganduje kawai ta sani, kuma ta aiko kwamitin zaɓe, wanda ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro suka tantance.

Abdullahi Abbas ya ƙara da cewa jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, sun duba yadda suka yi nasu zaɓen, amma INEC ba ta duba na su Ɗanzago ba.
Game da zargin ƙin biyan haraji, ya ce ya sa takardarsa ta shaidar biyan haraji a fom ɗin da ya miƙa wa uwar jam’iyya.

“Abin dariya ne ma a ce ban sa takardar shaidar biyan haraji ba a fom ɗina. Mun tabbatar da cewa mun bi duk wani sharaɗi na doka”, in ji Abdullahi Abbas.

Game da zargin ƙin ajiye shugabanci, Abdullahi Abbas ya ce ya ajiye shugabanci kwanaki 34 kafin zaɓe.

“Kodayake a matsayin shugaban riƙo ƙwarya, ba na buƙatar in ajiye shugabanci, amma don a yi maganin duk wani rashin bin doka, na ajiye shugabanci ranar 12 ga Satumba, 2021, wanda shi ne kwanaki 34 kafin zaɓe. To maganar me yake yi?”,

Takardar ajiye shugabanci da takardar shaidar biyan haraji da Daily Nigerian ta gani sun nuna iƙirarin Abdullahi Abbas yana da ƙanshin gaskiya.

Uwar jam’iyyar APC ta ƙasa ta ce zaɓen da kwamitocin zaɓen da ta kafa suka yi ne kawai za ta yadda da su.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan