El-Rufa’i Ya Wajabta Yin Allurar Riga-kafin COVID-19 A Kaduna

293

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce daga ranar 31 ga Oktoba, 2021, duk wanda yake son shiga duk wani ofishin gwamnatin jihar sai ya nuna shaidar riga-kafin corona da safar rufe hanci da baki.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mashawarcin Gwamnan Kaduna Kan Kafafen Watsa Labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar ranar Talata.

Mista Adekeye ya ce tuni Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna ta fara yi wa ma’aikatan gwamnatin jihar allurar riga-kafin COVID-19, aikin da za a kammala a ƙarshen Oktoba.

“Dole masu zuwa ofisoshin gwamnati su nuna katin riga-kafin corona.

“Duba da ƙarancin alluran riga-kafin, za a buƙaci waɗanda ba su nuna shaidar yin rijistar allurar riga-kafin da Ma’aikatar Lafiya ta ba su.

“Kwamishiniyar Lafiya, Dokta Amina Mohammed Baloni ta sanar da al’umma cewa su yi rijista a cibiyar kula da lafiya matakin farko mafi kusa da su domin hukumomi su samu sauƙin tuntubar su da zarar an kawo riga-kafin na COVID-19”, a cewar sanarwar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan