Likitoci Sun Ba Sarauniyar Ingila Shawara Ta Tafi Hutu

474

Sarauniyar Ingila, sarauniya mafi daɗewa a karagar mulki a duniya ta yanke shawarar tafiya hutu na ‘yan kwanaki bisa wata shawara da likitocinta suka ba ta.

Sarauniyar ta kuma soke kai ziyara Northern Ireland, a cewar Fadar Buckingham.

Fadar ba ta bayyana me ya sa Sarauniyar Ingilar za ta tafi hutu by, amma ta ce Sarauniyar ‘yar shekara 94 tana cikin ƙoshin lafiya.

Fadar ta ce a nan gaba kaɗan Sarauniyar za ta kai ziyara Northern Ireland ɗin.

A ranar Talata ne Sarauniyar ta karɓi baƙuncin manyan masu kuɗin duniya da suka haɗa da Bill Gates da Natarajan Chandrasekaran da kuma Firaministan Birtaniya, Boris Johnson a Windsor Castle gabanin wani taron ƙoli da za a yi mai taken COP26 Summit.

“Da ƙyar Sarauniya ta karɓi shawarar likitocin ta tafiya hutu na ‘yan kwanaki.

“Mai Martaba tana cikin ƙoshin lafiya kuma ba ta ji daɗi ba yadda ba za ta samu damar ziyartar Northern Ireland ba, inda aka shirya za ta yi abubuwa da yawa”, a cewar Fadar Buckingham.

Sarauniya Elizabeth ta shafe fiye kusan shekara 70 a karagar mulki. A lokacin da ta hau karagar mulki tana ‘yar shekara 25.
Sarauniya Elizabeth II ta hau karagar mulki ne ranar 6 ga Fabrairu, 1952, bayan mahaifinta ya rasu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan