Tawagar masu zanga-zanga sun fantsama wasu titunan Babban Birnin Tarayya Abuja ranar Laraba don tunawa da shekara ɗaya da gudanar da zanga-zangar #EndSARS.
Masu zanga-zangar dai sun taru ne a sansanin Unity Fountain da ke Abuja, kafin su fantsama kan tituna.
Jaridar Aminya ta rawaito cewa daga cikin masu zanga-zangar, har da mawallafin jaridar nan ta intanet, Sahara Reporters, Omoyele Sowore.
Sowore dai ya yi musu jawabi yayin da su kuma suke ɗauke da kwalaye.
Turawa Abokai