Wata Mata Ta Falla Wa Wani Ɗan Sanda Mari A Abuja

242

Wata mata mai sana’ar dafa abinci, Yengi Best, ta bayyana a gaba wata Kotu Mai Daraja ta 1 a Karu dake Abuja bisa zargin ta da falla wa wani ɗan sanda mari.

‘Yan sanda sun tuhumi Misis Best, ‘yar shekara 40 da yin sojan gona, amfani da ƙarfi ta hanyar da ba ta dace ba da kuma tsorata ma’aikatan gwamnati da nufin hana su gudanar da ayyukansu.

Ana kuma zargin ta da tayar da zaune tsaye.

Jami’an ‘yan sanda suna atisaye.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Osho Olanrewaju, ya shaida wa kotun cewa ranar 21 ga Agusta, wata tawagar ‘yan sanda bisa jagorancin Ayodele Stephen, masu aiki a Ofishin ‘Yan Sanda na Karu suka kama wanda ake zargin.

“A lokacin da ‘yan sanda suke ci gaba da gudanar da aikinsu a kusa da gidajen ma’aikatan ma’aikatar ƙasashen waje, Karu, suka kama wanda ake zargin a tsakar dare.

“A lokacin da ake bincike, wadda ake zargin ta ci zarafin ɗan sandan ta hanyar marin sa har sau biyu da kuma ji masa rauni.

“Wadda ake zargin ta yi iƙirarin cewa ita ma’aikaciyar tsaro ce da nufin tsorata ɗan sandan. Bayan nan ne sai ‘yan sandan suka kai maganar ga Ofishin ‘Yan Sanda na Karu”, in ji Mista Olanrewaju.

Mai gabatar da ƙarar ya ce wannan laifi ya saɓa da tanade-tanaden sashi na 132, 267, 252 da 113 na Penal Code.

Sai dai wadda ake zargin ta musanta aikata haka.

Alƙalin kotun, Inuwa Maiwada, ya bada belin wadda ake zargin akan kuɗi naira N500, 000 tare da kawo manyan mutane guda biyu.

Alƙali Inuwa ya ce dole mutane biyun su bada shaidar su su waye, kuma dole su bada adireshinsu ga Magatakardar Kotun.

Ya daga ƙarar zuwa ranar 28 ga Oktoba, 2021 don ci gaba da sauraro.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan