Mai Kamar Zuwa: Murtala Sule Garo shi ne zaɓin al’ummar jihar Kano a shekarar 2023

  504

  Alhaji Murtala Sule Garo, wanda aka fi sani da Kwamandan Yaƙi Na Baba Ganduje shi ne kwamishinan ma’aikatar da ke kula da ƙananan hukukomi da masarautu a jihar Kano, kuma shi ne tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kabo, kuma tsohon shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi reshen jihar Kano.

  Murtala Garo matashi ne jajirtacce, mai ra’ayin siyasar ƴan mazan jiya kamar irin su marigayi Malam Aminu Kano, Muhammad Abubakar Rimi da Malam Lawan Dambazau da sauransu da dama. Kuma gogaggen ɗan siyasa ne da ya kware wajen iya tafiyar da ragamar shugabancin al’umma.

  Masu sharhi da nazari akan al’amuran da su ka shafi siyasar jihar Kano na ganin idan har akwai wani mutum guda da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince da shi, kuma yake taƙama da shi a gwamnatinsa, to shi ne Alhaji Murtala Sule Garo.

  Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Murtala Sule Garo a gurin wani taro

  Hakan ba ya rasa nasaba da yadda alaƙa da mutuntaka da ke tsakanin marigayi Alhaji Sule Galadima Garo da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tun tsahon shekaru. Haka kuma dangantaka ta ƙara ƙarfi ne tsakanin Murtala Garo da Dakta Abdullahi Umar Ganduje a lokacin da shi Murtalan ke shugabantar ƙaramar hukumar Kabo, inda shi kuma Ganduje ke riƙe da muƙamin mataimakin gwamnan jihar Kano, kuma kwamishinan ƙananan hukumomi a jihar.

  Alhaji Murtala Sule Garo

  Alhaji Murtala Sule Garo ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar Kano wato ALGON, kuma a lokacin da ya rike da wannan muƙami an ga yadda ya haɗa kan shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano guri guda inda su ka samarwa da al’ummar da su ke shugabanta managartan ayyukan raya ƙasa da kuma cigaba mai ɗorewa.

  Tasiri Da Farin Jinin Murtala Sule Garo A Siyasar Jihar Kano

  Masu iya magana na cewa siyasar Kano sai Kano, kuma a ko da yaushe ta kan zo da wani abu sabo, a wannan lokacin tuni tauraruwar Murtala Sule Garo ta fara haskawa a fagen siyasar Kano, inda ya ke samun goyon baya daga ɓangarorin al’umma daban-daban. Haka kuma tarihi ya nuna yadda tasirinsa ya yi karfi a mahifarsa ta Garo a lokacin da ya tsunduma harkokin siyasa, inda kafatanin al’ummar wannan yanki su ka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Kabo.

  A lokacin da ya ke shugabancin ƙaramar hukumar Kabo ya yi ayyuka masu yawa waɗanda su ka shafi rayuwar talaka kai tsaye, musamman a ɓangaren da ya shafi bunƙasa harkokin ilimi da kiwon lafiya da baiwa mata da matasa jari domin dogaro da kai, da farfaɗo da harkokin noman rani da na damuna ta hanyar samarwa da manoma iri da takin zamani da sauran abubuwa masu amfani ga rayuwar jama’a.

  A matakin siyasar jihar Kano, Murtala Sule Garo ya kasance a matsayin sahun farko wanda tauraruwar sa ta ke haskawa, domin kafatanin kafafen yaɗa labarai musamman gidajen rediyon da su ke shirye-shiryen siyasa babu sunan ɗan siyasar da ke shan ambato da nuna goyon baya tamkar Murtala Sule Garo.

  Haka kuma a bayyane ta ke kafatanin shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano su 44 sun amince tare da nuna goyon bayansu ga Alhaji Murtala Sule Garo, wanda hakan ne ya haifar da rundunar siyasa mai ƙarfin a jihar Kano wacce ta ke goyon bayan Kwamanda Murtala.

  Murtala Sule Garo da Shugaban karamar hukumar Birnin Kano Fa’izu Alfindiki

  A ɗaya ɓangaren kuma jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da jihar Kano, cike take da masu buƙatar neman kujerar gwamnan jihar Kano a shekarar 2023.

  Sai dai inda gizo ya ke saƙar shi ne kaf cikin jerin masu neman wannan buƙatar babu wanda ya ɗara Alhaji Murtala Sule Garo dacewa da cacantar ɗarewa kujerar Gwamnan Kano, bisa manyan dalilai kamar haka:

  • Alhaji Murtala Sule Garo mutum ne mai kyakkyawar mu’amala tsakaninsa da al’umma.
  • Matashin ɗan siyasa ne shi da ke girmama Malamai da Attajirai.
  • Matashin ɗan siyasa ne da ya ke girmama ƴan kasuwa da masu ƙananan masana’antu.
  • Murtala Sule mutum ne da ya san darajar ma’aikatan gwamnati da mutunci su.
  • Murtala Sule Garo mutum ne da ya san darajar Mata da Matasa domin babban burinsa shi ne ganin kullum sun samu abin da za su dogara da kan su, wanda hakan ne ya sanya shi da mai ɗakin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje wato Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ke zagayen ƙananan hukumomin jihar Kano guda 44 domin baiwa mata jarin sana’a domin dogaro da kai.
  • Murtala Sule Garo mutum ne mai kishin jihar Kano da Kanawa.
  • Murtala Sule Garo ɗan siyasa ne da baya rigima da kowa a da’irar siyasar jihar Kano.
  • Murtala Sule Garo ɗan siyasa ne da kullum kofarsa a buɗe ta ke wajen taimakon al’umma.
  • Haka kuma Murtala matashi ne mai kishin Ilimi da ganin ya bunƙasa a jihar Kano.
  • Wani abin armashi shi ne yadda Murtala Sule Garo ke da kishin ganin harkokin noma sun farfaɗo a jihar Kano, har ta kai ga jihar na gogayya da manyan ƙasashen duniya a wannan ɓangaren.

  Tabbas al’ummar jihar Kano za su bayar da shaida akan waɗannan kyawawan halaye na Alhaji Murtala Sule Garo mai taken Kwamandan Yaƙi Na Baba Ganduje. Wanda hakan ne ya sanya tuni jama’a daga ɓangarori daban-daban su ke ƙara nuna goyon bayansu ga Alhaji Murtala Sule Garo, domin ya zama magajin gwamna Abdullahi Umar Ganduje a shekarar 2023.

  Haƙiƙa Murtala Garo matashi da zai kai jihar Kano gaci tare da ɗorawa daga taswirar da gwamnan jihar Kano na farko marigayi Audu Bako ya samar. Domin an sha jin gwamna Abdullahi Umar Ganduje na cewa Murtala Sule Garo kwamishina ne da ya yi zarra, yana mai bayyana shi a matsayin kwamishinan da ya yi wa dukkan shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano adalci ba tare da nuna bambanci ba.

  Kwamandan Murtala Sule Garo

  Babbar addu’ar al’ummar jihar Kano da su ka haɗa da Malamai da Ƴan Kasuwa da Ƴan Boko da Matasa da Mata da kuma ƴan Jam’iyyar APC ita ce Allah ya kaimu shekarar 2023 lokacin da za a rantsar da Alhaji Murtala Sule Garo a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano.

  Muhammad Abba mai sharhi ne akan al’amuran yau da kullum ya rubuto daga Kano. 08064230122

  Turawa Abokai

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan