Karon Farko Malam Ibrahim Khalil ya Magantu Tun Bayan da aka yi Yunƙurin Tsigeshi

366

Shugaban majalisar malamai ta Kano Sheikh Ibahim Khalil, ya bayyana rikicinsa da malaman da suka yi yunƙurin tsigeshi a matsayin wata jarrabawa daga Allah.

Ibrahim Khalil ya bayyana hakanne ya yin da ya karɓi baƙuncin mambobin majalisar ƙolin addinin musulunci ta ƙasa da suka ziyarce shi a ofishinsa ranar Asabar.

Malamin ya ce Allah ya yi alƙawarin jarraba bawansa don a ga ko zai iya jurewa ko akasin haka

“Allah Ya yi alkawarin jarraba mu a kowanne abu. Abin da ya faru wataƙila Allah Ne Ya yi niyyar jarraba mu don Ya ga ko da gaske muke a tafarkinsa.

Saboda haka, na ɗauki wannan a matsayin jarrabawa, amma Alhamdulillahi, Allah ya nuna mana tsintsiya maɗaurinki ɗaya muke, kuma ina rokon ya yafe mana.

“Ina godiya ga dukkan waɗanda suka tsaya tsayin daka wajen ganin kan malaman Kano ya haɗu, ciki har da waɗanda ma ba sa cikin majalisar, amma suna mana fatan alheri,” inji Sheikh Khalil.

Anasa jawabin Malam Jamilu Mu’azu Haidar, a madadin malaman ya ce sun zo Kano ne don nuna goyon bayansu ga shugabancin nasa.

Malam Jamilu, ya ce sun saurari bayanai daga malaman Kano daban-daban, inda aka ba su tabbacin cewa babu hannun gwamnatin jihar Kano a rikicin.

“Muna kira ga sauran malamai da su ji tsoron Allah su dawo a ci gaba da tafiya tare, ƙarƙashin Sheikh Khalil, kamar yadda ake a baya,” inji Malam Jamilu.

Idan za a iya tunawa dai a baya-bayan nan ne wasu guggun malamai a Kano suka gudanar da wani taron manema labarai tare da sanar da tsige Malam Ibrahim Khalil daga muƙaminsa.

Inda kuma nan take suka naɗa Farfesa Abdallah Saleh Fakistan a matsayin wanda zai maye gurbinsa, lamarin da samu tutsu a wajen jama’a dama sauran malamai.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan