SHAHARARREN mawaƙin nan kuma ɗan siyasa, Alhaji Dauda Adamu Kahutu (Rarara), ya bayyana cewa lallai maganar da ake yawo da ita ta batun tsayawar sa takarar zama ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Bakori da Ɗanja da ke Jihar Katsina gaskiya ce.
Rarara da kan sa ya tabbatar wa da mujallar Fim haka a Katsina a wata zantawar da ta yi da shi a kan wasu batutuwa da su ka shafi waƙoƙin sa, musamman waƙar da ya ce talakawa ne su ka biya kuɗin yin ta da kuma batun tsayawar sa takara.
Ya ƙara da cewa ya zuwa yanzu akwai batun sabuwar waƙar da ya yi wadda talakawa su ka biya kuɗi domin bayyana ayyukan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Ya ce kwanan nan zai tsunduma zagaya jihohin Nijeriya domin nuna irin ayyukan da ya gano Buhari ya yi.

Ya ce, “Idan Allah ya sa na kammala wannan aikin da ke gaba na, to zan tsaya takarar ɗan Majalisar Tarayya na Ƙananan Hukumomin Bakori da kuma Ɗanja. Idan kuma wannan aiki ya sha gaba na, sai kuma a duba batun nan gaba.”
A cewar Rarara, ya yi niyyar gano ayyukan Shugaban Ƙasa guda 90 amma sai ya gano 900,000 wanda ya ke ganin aikin ya na da yawa, amma dai idan ya samu damar kammala wannan aikin zai dawo kan batun yin takarar sa wanda tuni ya fara yawo a gidajen siyasa.
Rarara ya bayyana cewa zaɓen shugabannin siyasa da aka gudanar a makon jiya a Katsina ya yi masa kyau, kuma ya yi yadda ake so, saboda haka ya na fatan wannan zaɓen zai taimaka wajen ƙara samun nasarar jam’iyyar su ta APC a zaɓe mai zuwa.
Bugu da ƙari, mawaƙin ya yaba da irin tsarin da aka bi wajen samar da shuwagabannin, ya ce abin ya yi matuƙar burge shi, kuma a Nijeriya babu inda aka yi abin da ya dace kamar Jihar Katsina.

Ya ce hatta Shugaban Ƙasa ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Aminu Bello Masari a kan haka.
Rarara ya ce, “Idan ka duba da kyau, tun daga zaɓen shuwagabanni na matakin rumfuna da ƙananan hukumomi da na jiha babu wanda ya ce bai yarda da tsarin da aka bi ba, saboda haka wannan shi ne ake kira shugabanci.
“Masari ya yi matuƙar ƙoƙari wajen haɗa kan ‘yan jam’iyyar APC a Jihar Katsina.”