Zan Tsaya Takarar Ɗan Majalisar Wakilai A 2023— Rarara

294

Shahararren mawaƙin siyasar nan dake Arewacin Najeriya, Dauda Adamu Kahutu da aka fi sani da Rarara, ya ce maganar da ake yawo da ita cewa zai tsaya takara a 2023 gaskiya ce.

Rarara ya ce tabbas zai tsaya takarar ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Bakori da Ɗanja da ke Jihar Katsina.

Ya bayyana haka ne a lokacin wata hira da mujallar Film Magazine ta yi da shi.

Daga hagu, Baban Cinedu, Dauda Adamu Kahutu Rarara da kuma Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Rarara ya ce kwanan nan zai tsunduma zagayen jihohin Nijeriya domin nuna irin ayyukan da ya gano Buhari ya yi.

“Idan Allah ya sa na kammala wannan aikin da ke gabana, to zan tsaya takarar ɗan Majalisar Tarayya na ƙananan hukumomin Bakori da kuma Ɗanja.

“Idan kuma wannan aiki ya sha gabana, sai kuma a duba batun nan gaba”, in ji shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan