Rayuwa ta tsananta a ƙasashe da yawa na duniya musamman ƙasashe matalauta. Hakan ya sa ‘yan ƙasa su na matukar kokawa da “gajiyawar” shugabanninsu, su na zanga-zanga, wasu ma su na fatan kawar da wadannan shugabanni ko ta halin ƙaƙa. Wannan ne ya ke sakawa idan aka sami juyin mulki (kamar yadda ya faru a Mali da Guinea da Sudan) sai ka ga ‘yan ƙasa an fito ana ta murna, tunaninsu an sami sabuwar gwamnati wacce za ta inganta rayuwarsu ta kawo karshen halin kunci da su ke ciki.
Sai dai kuma a mafi yawan lokaci su kan su sababbin shugabannin al’amura su na fin karfinsu har su ma a koma ana zarginsu da gajiyawa su ma ana fatan kaucewarsu kamar yadda ya faru a Mali da Sudan.
A fahimtata kafafen yaɗa labarai musamman na waje su na taimakawa wajen hura wutar kiyayya tsakanin ‘yan Africa da shugabanninsu. Misali kowa ya san cewa har a ƙasashe masu arziki yanzu haka an samu canjin rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki. A London an yi mummunar wahalar fetur. A America yanzu haka ana tsoron samun “hyper-inflation” wato rubanyawar farashi nunki-ba-nunki. Idan ka na bibiyar labarai za ka ga yadda wadannan kafofi su ke kokarin ɗora halin da ake ciki akan Covid-19 wacce ta kusa durkusar da tattalin arzikin duniya. Sannan za ka ga su na rawaito kokarin da shugabanninsu su ke wajen tinkarar matsalar illa iyaka su nuna kokarin ya kai a yaba ko bai kai ba. Amma idan Africa ne za ka ga kai tsaye za su danganta matsalar da gajiyawar shugabanni ko da sun san cewa abin ya fi karfinsu kuma ba za su damu wajen nuna irin kokarin da shugabannin su ke yi ba. A haka kafofin labarai na gida su ma za su rawaito sannan jahilan masu sharhi su yi ta hayaniya da sunan wai su masana.

Alhamdulillahi, mu anan Dimokuraɗiyya ta fara ƙarfi da wahala ka ji wani mai hankali ya na fatan juyin mulki. Kusan kowa ya na jiran lokacin zaɓe ne don yin abinda ya ke gani ya dace da kuri’arsa. Wannan babban cigaba ne. Inda gizo ya ke sakar kawai shi ne da yawa ba ma damuwa wajen jinjina wadanda mu ke so mu zaba sannan idan mun zaɓe su wanne irin taimako da haɗin kai su ke buƙata daga garemu.
Duk wanda ya san irin lalacewar da ƙasar nan ta yi ya san da wahala wani mahaluki ya iya gyarata ba tare da an taimaka masa ba. Da yawa wata lalatar har mutum ya bar mulki ba zai san da ita ba kuma ko ya san da ita shi ba Allah ba ne mai iko akan komai. Zai yi iya abinda zai iya ne kawai ko an gamsu ko ba a gamsu ba.
Ya Allah ka ba mu shugabanni na gari, ka nuna musu daidai kuma ka ɗora su a kanshi, mu kuma ka ba mu ikon yin hakuri da su da taimaka musu ta kowacce hanya da za mu iya.
Allah ka fitar da kasarmu Nigeria da ma duniya baki daya daga halin kunci, takura da tsadar rayuwa da ake fama da shi a wannan lokaci.
Dakta Ibrahim Siraj Adhama malami a tsangayar sadarwa da harkokin aikin jarida da ke jami’ar Bayero da ke Kano.