Jami’an tsaro sun bankaɗo masana’antar ƙera muggan makamai a Jos

523

Kafar RFI da rawaito cewa mahukuntan Najeriya sun ce sun gano wata ma’aikata da ake ƙera bindigogi ƙirar AK-47 a garin Jos, a jihar Filato kuma yanzu haka an kwashe bindigo da aka ƙera tare da cafke manajan ma’aikatar. Hakan ya zo ne a lokacin da ƙasar takee fuskantar ƙalubalen tsaro, a sakamakon yawaitar ƙanana da manyan makamai a cikin ƙasar nan.

Duk da cewa babban sufeto janar na ‘yan sandan, Malam Usuman Alƙali Baba, bai bayyanawa majiyar TDR Hausa sunan mutumin ko inda ya fito ko kuma wa yake sayarwa da makaman ba, amma dai ya bayyana cewa tuni an kwashe bindigogin. Ya ƙara da cewa bindigogin, bindigogi ne masu hatsari, kuma mutanen da aka kama suna ƙera su ne kamar ƙirar asali.

Jihar Filato dai tana ɗaya daga cikin jihohin Arewa da aka fi samun rikicin addini da kuma rikicin ƙabilanci a sakamakon yadda wasu mazaunan garin suke yi wa wasu kallon baƙi waɗanda ba su cancanci zaman jihar ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan