Kimanin shaguna uku ne suka ƙone ƙurmus tare da Samun a sarar rayukan da ba’a kai ga tantance su ba a yayin da tankar man fetur ta kama da wuta a jihar Naija
Lamarin ya farune a ranar Lahadi, 31 ga Oktoba, 2021 a yankin garin Enagi, inda wasu tankokin man fetur 2 suka ci karo da juna kuma suka kama da wuta.

Inda iftila’in ya yi sanadiyyar a ƙalla ƙonewar shaguna 3 tare da samun rasa rayukan da ba a kai ga tantan cewa ba kamar yadda shaidun gani fmda ido su ka shaida.

Wasu dake yankin sun hau shafukan sada zumunta inda suke ta Alhinin abinda ya faru.

Sai dai harzuwa kammala wannan rahoton Hukumar kashe gobara dake yankin bata ba tace komai ba kan wannan iftila’i.

Turawa Abokai