Ranar kare haƙƙin ƴan jarida ta duniya: Jerin ƙasashe 11 da ƴan jarida ke fuskantar uƙuba

282

Hukumar bunƙasa ilimi da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta ware ranar ranar 2 ga Nuwamba a matsayin ranar kare hakkin ‘yan jarida a duniya. An ware ranar ne domin kiran kawo karshen karkashe ƴan jarida da ake yi a faɗin duniya.

An ayyana ranar ne don kira ga kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya, musamman hukumar raya al’adu ta Majalisar wato UNESCO domin kare ‘yan jarida daga hare-hare a yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Haka kuma a duk lokacin da aka samu an aikata laifi kan ‘yan jarida da ya kunshi cin zarafi ko kisa, UNESCO na bukatar a tabbatar da an gurfanar da masu laifin don hukuntasu.

Wata kididdiga da wata kungiya mai fafutukar kare hakkokin ‘yan jarida wato CPJ mai mazauni a birnin New York na Amurka, da ta ke fitarwa a duk shekara ta yi nazari kan kasashe 11 da ake kashe ‘yan jarida kuma ba tare da an hukunta wadanda suka aikata laifin ba a duniya.

Somalia ce a matsayi ta 1 da ake kashe ‘yan jarida ba tare da an hukunta wadanda suka aikata laifin ba.

An kiyasta cewa daga shekarar 2006 zuwa 2017 an kashe kusan ‘yan jarida 1,010 a dalilin ayyukan da suke gudanarwa a fadin duniya.

Sannan kashi 9 cikin 10 na irin wannan kashe-kashe na wucewa ne ba tare da an hukunta wadanda suka aikata al’amarin ba, abin da ke kara sanya rayukan ‘yan jarida cikin hadari.

Jerin ƙasashen duniya da ƴan jarida ke fuskantar uƙuba

Jama’a da dama sun yi amannar ƴan jarida na taka rawa wajen bankado irin ta’asa da cin hanci da rashawar da ake zargin wasu shugabanni na aikatawa, tare da kawo sauyi a kasashen da gwamnatocinsu ba sa bin tsarin demokradiyya.

Sai dai a yayin da ake bikin ranar ƴancin ƴan jarida ta duniya, aikin jarida a wasu daga cikin kasashen duniya ya kasance tamkar aikata mugun laifi ne, inda hukumomi ke yiwa kafofin yada labaru bita-da-kulli da capke ‘yan jarida a wasu lokutan ma har ta kai ga kisa. Jerin ƙasashen su ne kamar haka:

Somalia,
Syria,
Iraq,
Afghanistan,
Mexico,
Philippines,
Brazil,
Pakistan,
Russia,
Bangladesh,
India.

Tambayar dai ita ce shin ko a ƙasashe masu tasowa kamar Najeriya ƴan jarida na da ƴancin gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata, wace rawa ya kamata su taka wajen karfafa tsarin dimokradiyya?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan