Yan bindiga sun kai hari gidajen malaman jami’ar Abuja

405

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari rukunin gidajen malaman jami’ar Abuja da ke yankin Giri a unguwar Gwagwalada.

A lokacin harin da ƴan bindigar su ka kai a safiyar yau Talata, sun yi awon gaba da Farfesa Obansa Joseph, da ke koyarwa a sashen ilimin tattalin arziki da tanadi na jami’ar tare da ya’yansa guda biyu.

Tuni mai magana da yawun jami’ar Habib Yakoob ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ƙara da cewa kimanin mutum shida ne ƴan bindigar su ka yi awon gaba da su

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan