Za A Samu Rana Da Hazo A Kwanaki 3 Masu Zuwa A Jihohin Najeriya— NiMet

530

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen cewa za a samu ƙwallewar rana da hazo daga ranar Talata zuwa Alhamis na wannan mako.

Rahoton yanayi da NiMet ta fitar ranar Litinin a Abuja ya yi hasashen cewa za a samu rana da hazo a yankin Arewa ranar Talata.

Hukumar ta yi hasashen cewa za a samu washewar sararin samaniya a yankin Arewa da kuma tsawa a yankunan Taraba da Kudancin Kaduna da safe.

A cewar hukumar, za a samu ƙura tare da hazo daga tazarar kilomita 3 zuwa a jihohin Kano, Katsina, Jigawa, Yobe da Borno a lokacin.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan