Kano: Kotu Ta Garƙame Wani Mutum Bisa Zargin Muzanta Ganduje

337

Wata Kotun Majistire mai zama a unguwar Nomansland, ta bada umarnin garƙame wani ɗan siyasa mai suna Mu’azu Magaji Ɗanbala, bisa zargin sa da ɓata wa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje suna.

Ana zargin Mu’azu da ɓata wa Gwamna Ganduje da ‘ya’yansa biyu, Abdul’aziz da Balaraba suna a Facebook.

Akwai wani mutumin da ake zarg mai suna Jamilu Shehu, amma bai bayyana a gaban kotun ba.

Laifukan da ake zargin mutanen da aikatawa sun haɗa da haɗa baki don aikata laifi, cin zarafi da gangan, tada hankalin jama’a da ɓata suna, laifukan da sun saɓa da Sashin na 97, 114, 391 da 399 na Penal Code.

A cewar Rahoton Bayanai na Farko, FIR, a ranar 26 ga Oktoba, 2021, Shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa, Auwal Lawal Shuaibu, ya shigar da ƙorafi ga Hukumar Adana Bayanan Sirri ta Jihar Kano, SIB, akan Muazu da Jamilu, mazauna ƙauyen Sabon Garin Ƙiru, dake ƙaramar hukumar Ƙiru a Jihar Kano.

“Cewa a wannan rana ku biyu kuka haɗa baki kuka yi wallafa a dandalin Facebook wadda ta shafi kima da muhibbar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano da ‘ya’yansa, Abdulaziz Ganduje da Balaraba Ganduje, inda kuka rubuta ɓalo-ɓalo ‘Ɓarayin Kano’, kuma kun sani sarai cewa abin da kuka yi zai iya haifar da rikici a jihar nan da ma waje.

“Saboda haka ana zargin ku da aikata waɗannan laifuka na sama”, a cewar FIR ɗin.

Sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata haka, kuma lauyansa ya roki kotu ta bada shi beli.

Amma lauyan mai ƙara, Wada Ahmad Wada ya soki buƙatar bada belin.

Alƙalin da zai saurari ƙarar, Aminu Gabari ya umarci Sashin Binciken Manyan Laifuka, CID, td ya gabatar da kundin ƙarar ga kotun don ta duba yiwuwar bada belin.

Ya bada umarnin a ajiye wanda ake zargin a gidan gyaran hali har lokacin da kotun za ta karɓi kundin ƙarar.

Kotun ta ɗaga ƙarar zuwa 8 ga Nuwamba, 2021 don ci gaba da sauraro.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan