Jam’iyyar APC a jihar Kano da ke Najeriya na ci gaba da fama da rikicin cikin gida, wanda ya samo asali tun kafin gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar a matakin mazabu da jiha da aka aiwatar baya bayan nan.
Tun da farko dai Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau da takwaransa na Kano ta Arewa da sauran wasu ƴan majalisun wakilai guda huɗu ne suka gudanar da wani taro na musamman inda suka yanke shawarar lallai dole shugabancin jam’iyyar ta APC ya takawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje birki kafin lamura su ƙarasa dagule.
Bayan kammala taron ne ɓangaren Sardaunan Kano da na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje su ka gudanar da zaɓukan jami’yyar a matakin jiha.

Ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje su ka zaɓi Alhaji Abdullahi Abbas Sanusi a matsayin shugaban jam’iyyar, yayin da ɓangaren Malam Ibrahim Shekarau su ka zaɓi Alhaji Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyyar ta APC.
Tasirin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje A Siyasar Kano
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ɗan siyasa ne kuma tsohon gogaggen ma’aikacin gwamnati. Masanin mulki a ilimance da a aikace, ya yi kwamishina har sau biyu, sannan kuma ya yi mataimakin gwamna shi ma sau biyu da sauran wasu muƙamai yanzu kuma yana matsayin gwamnan Kano.
Da yawan mutane na kallon Ganduje a matsayin mutum ne shi mai haƙuri da kawaici da kuma biyayya ga duk wanda ya grime shi ta kowacce fuska wanda ka iya kasancewa girma na shekaru ko na harkar aiki. Sai dai kuma makusantansa da abokan siyasarsa na yi masa shaidar rashin tsayawa akan magana ɗaya musamman a al’amuran da su ka shafi siyasa.
Gwamna Abdullahi Umar ya fara siyasa tun a jamhuriya ta biyu, inda ya shiga jama’iyyar National Party fo Nigeria (NPN). A wannan jama’iyyar ya riƙe muƙamin mataimakin sakatare na jihar Kano daga 1979 zuwa 1980. Ya sake shiga jama’iyyar PDP a shekarar 1999, ya kuma canja sheƙa tare da gwamnansa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, inda suka fice daga jama’iyyarsu ta PDP suka koma sabuwar jama’iyyar haɗaka ta APC, wanda a ƙarƙashin tutar wannan sabuwar Jama’iyyar ya samu nasarar cin zaɓensa na gwamna.
Tarihin siyasar Abdullahi Umar Ganduje ya nuna cewa ya tsaya takarar Kujerar Gwamnan jihar Kano a shekarar 1999, inda daga baya aka yi musu sulhu ya janye ya barwa tsohon Gwamna Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda shi kuma daga baya ya ɗauke shi a matsayin mataimakinsa.
Bayan kammala wa’adin mulkin gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso a shekarar 2015, Abdullahi Umar Ganduje, ya sake tsayawa takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin tutar jama’iyyar APC. Ya kuma yi nasara kan abokin adawarsa a babban zaben, Malam Salihu Sagir Takai da kuri’a 1,546,434 yayin da Takai ya samu kuri’a 509,726 a zaɓen 11 ga watan Afrilun 2015.
Sai dai duk da wannan tarihin siyasar na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, masu sharhi akan al’amuran da su ka shafi siyasar Kano na yi masa kallon ɗan siyasar da ba shi da gida na kan sa. Haka kuma ana kallon waɗanda su ke zagaye da shi su na binsa ne kawai domin yana rike da mulki.

Wani abin da masu sharhin ke ƙara buga misali da shi game da Gandujen shi ne mafi yawan waɗanda su ke cikin gwamnatinsa su na da ra’ayin Kwankwasiyya ko kuma ba sa tare da Gandujen ɗari bisa ɗari, musamman idan aka yi la’akari da yadda jami’an gwamnati da ƴan Gandujiyya su ka gaza taɓuka komai a lokacin zaɓen shekarar 2019, inda lamarin ya kai gwamnan shiga zaɓe zagaye na biyu.
Wani ƙarin misalin shi ne yadda gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gaza samun cikakken goyon al’ummar ƙaramar hukumarsa ta haihuwa wato Dawakin Tofa, domin mafi yawan al’ummar wannan ƙaramar hukuma musamman matasa ba sa tare da shi a harkokin siyasa.
Su Wanene Su Ke Tare Da Ganduje?
A zahiri babu wani ɗan siyasa da ke da jama’a a jihar Kano kamar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, domin shi ke da mafi yawan ƴan majalisar dokokin jihar Kano da kwamishinoni da ƴan majalisar wakilai da Sanata guda ɗaya (Kabiru Ibrahim Gaya), da shugabannin ƙananan hukumomi da Kansiloli da kuma masu ba shi shawara.
Haka kuma yana da ƙarfin gwamnati wanda ba wasa ba ne, domin ta na da matuƙar ƙarfi da tasiri akan dukkanin wani abu da ta sanya a gaba. Amma kaso mai yawa na waɗanda su ke tare da Gandujen da masu riƙe da muƙaman siyasa sun kasance masu fuska biyu. Ma’ana a zahiri su na tare da Gandujiyya a ɗaya ɓangaren kuma su ne ke mata zangon ƙasa wanda hakan babbar matsala ce a harkokin siyasa har da rayuwa gaba ɗaya.
Tasirin Malam Ibrahim Shekarau A Siyasar Kano
Malam Ibrahim Shekarau, tsohon malamin makaranta ne kuma masanin fannin karantarwa da harkar ilimi, gogaggen ma’aikacin gwamnati kuma fitaccen ɗan siyasa, mutum ne shi mai haƙuri da sauƙin hali da kirki da kuma biyayya ga duk wanda ke gaba da shi, a shekaru ko kuma a mulki, wanda hakan ya ba shi ɗimbin magoya baya a jihar Kano da ma wasu sassan Arewacin Najeriya.
A lokacin da Malam Ibrahim Shekarau ya shigo cikin siyasar jihar Kano gadan – gadan ba’a ɗauke shi a matsayin wani ɗan takara da zai yi tasiri ba a zaben gwamnan da aka yi a shekarar 2003 a jihar, amma daga baya kuma sai ya yi tasiri inda ya lashe zaɓen.
Lashe wannan zaɓen da Malam Shekarau ya yi ya jawo hankalin al’ummar Najeriya tare da jefa mamaki akan yadda Malamin makaranta da ke jam’iyyar adawa ya kayar da gwamna mai ci.
A ɓangare guda kuma Malam shekarau ɗin ya kafa tarihi inda ya zama gwamna na farko da aka zabe shi a karo na biyu a matsayin gwamna a tarihin jihar Kano.

Salon mulkin Malam Ibrahim Shekarau a lokacin da ya ke mulkin jihar Kano, salon gwamnati ne da ya haɗa dukkanin bangarorin al’umma. Domin a lokacin da ya ke gwamnan Kano ya baiwa ƙananan hukumomi haƙƙinsu ta yadda arziki ya wadata a tsakankanin al’ummar jihar Kano. Ya shigo da Sarakuna da Malamai da Ƴan boko da talakawan jihar Kano cikin gwamnatinsa.
Wannan salon gwamnatin Malamin gwamnan ta janyo masa farin jini daga ɓangarori daban-daban na al’umma. Domin a lokacinsa ko masu ƴan jam’iyyar adawa sai da su ka tsuke bakinsu saboda suma an tsoma su a cikin gwamnati.
Su Wanene Su Ke Tare Da Malam Shekarau A Siyasar Kano?
Malam Ibrahim Shekarau a siyasar jihar Kano yana da tasiri ƙwarai da gaske musamman a tsakankanin ma’aikatan gwamnati a matakin jiha da ƙananan hukumomi. Haka kuma a kafatanin ƙananan hukumomin jihar Kano 44 babu inda babu masu ra’ayin siyasar Malam Ibrahim Shekarau na haƙiƙa wadanda su ke yi ba domin kuɗi ba sai domin aƙida da yarda siyasar Malamin.
A ɗaya ɓangaren kuma gidan siyasar Sardaunan Kanon ya ƙara ƙarfi a sakamakon dawowar Sanata Kano ta Arewa, Sanata Barau Ibrahim Jibrin da Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Rimin Gado da kuma Tofa da Barista Haruna Isa Dederi ɗan majalisa mai wakiltar Karaye da Rogo da Nasiru Abduwa Gabasawa da Sha’aban Ibrahim Sharada da wasu daga cikin ƴan majalisar dokokin jihar Kano, wanda har yanzu ba su filto fili sun jaddada goyon bayansu ga tafiyar Malam Ibrahim Shekarau ɗin ba.
Baya ga wadannan ƴan majalisun akwai fitattun ƴan siyasar da aka san su akan tsayawa akan ra’ayin abin da su ka yi imani da shi a fage irin na siyasa. Wasu daga cikin wadannan ƴan siyasa ana yi musu kallon masu ra’ayin ƴan mazan jiya da su ka ƙware wajen rigimar siyasa. Fitattu daga cikinsu akwai Alhaji Ahmadu Haruna Zago da Abdulmajid Danbilki Kwamanda da Alhaji Shehu Ɗalhatu, da Alhaji Murtala Alhassan Zainawa da Kwamared Alhassan Uba Idris da kuma Alhaji Sharu Baban Lungu.

Tabbas wannan shata layi da ɓangarorin biyu su ka yi a cikin jam’iyyar APC zai iya zama dalilin wargaza jam’iyyar tsintsiya, wanda kuma hakan kan iya haifar da gaza lashe madafun iko a zaɓen shekarar 2023 a jihar Kano.
Lokaci shi zai tabbatar da wanene zai yi nasara a wannan kokawar siyasar!