‘Yan Majalisar Tarayya Na Kano Na Yin Amaja A Ayyukan Mazaɓu— Rahoton ICPC

394

Hukumar Hana Cin Hanci da Dangoginsa Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, ICPC, ta gano cewa wasu ‘yan Majalisar Tarayya na Jihar Kano ba sa gudanar da aikin mazaɓu yadda ya kamata.

ICPC ta gano cewa daga cikin ayyukan mazabu 104 na jihar Kano, an yi amaja a ayyuka 16, yayin da aka yi watsi da guda uku.

‘Yan kwangila 79 ne su ka gudanar da ayyukan, kuma tuni an buƙaci tara daga cikinsu da su dawo bakin aiki sakamakon rashin ingancin ayyukan da su ka yi.

ICPC ta ce ‘yan majalisar da su ka fi yin amaja a ayyukan mazaɓu su ne Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, Mustapha Bala Dawaki, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Dawakin Kudu/ Warawa da Muktar Mohammed, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kura/ Madobi/ Garun Malam.

“Sanata Barau Jibrin shi ne ya fi yin aikin mazaɓa mafi inganci”, in ji ICPC.

Ayyukan da ‘yan majalisar su ka yi sun haɗa da gina azuzuwa, samar da fitilun kan titi masu amfani da hasken rana da kuma rarraba tiransifoma, kamar yadda ICPC ta bayyana.

“Muna buƙatar goyon bayan al’umma wajen sa ido a waɗannan ayyuka, musamman aikin samar da ƙaramar tashar lantarki a Bici”, in ji ICPC.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan