Ƙungiyoyin mata a Kano sun nuna goyon bayansu ga tafiyar A.A Zaura

250

A jihar Kano wakilcin ƙungiyoyin mata daga ƙananan hukumomi 44 sun jaddada goyon bayansu ga tsarin tafiyar siyasar Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura wanda aka fi sani da A.A Zaura. Ƙungiyoyin matan sun bayyana hakan ne a wata ziyara ta musamman da su ka kaiwa fitacciyar yar siyasar nan kuma jigo a cikin jam’iyyar APC, Hajiya Maryam Umar Kofar Mata a ofishinta da ke Kano.

Matan sun bayyana cewa lokaci yayi da ya kamata ɗaukacin matan jihar Kano su fito fili domin bayyana matsayar su ga al’ummar jihar Kano akan wanda ya kamata su marawa baya a cikin jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2023 da ke tafe.

Hajiya Hassana Gwamna wacce ɗaya ce daga cikin wakilan ƙungiyoyin matan ce ta bayyanawa wakilin Labarai24 cewa sakamakon irin ƙoƙarin da Hajiya Maryam Umar Kofar Mata ke yi akan tafiyar A.A Zaura ya sanya su ka yanke shawarar nuna goyon bayansu ga Zauran.

“Irin ƙoƙari da ɗawainiyar da Hajiya Maryam Kofar Mata ta ke yi da mata a jihar Kano, musamman wajen ba su jari da tallafa musu ya sanya mu ka ɗauki wannan matakin”.

“Kuma tun asali mu mata a jihar Kano muna biyayya da dukkanin wani tsarin siyasa da Hajiya Maryam ta ke tare da shi, dan haka babu gudu ba ja da baya a wannan tafiya ta A.A Zaura”

Ita ma Hajiya Binta P. A da ta kasance ɗaya daga cikin matan da su ka yi jawabi a lokacin ziyarar cewa ta yi a jihar Kano babu wata yar siyasa mace da ke kyautatawa mata da kuma ganin rayuwarsu ta inganta kamar Hajiya Maryam Umar Kofar Mata.

“Hajiya Maryam ta bamu jari ta taimakemu domin rayuwarmu mata a jihar Kano ta inganta. A saboda haka daukacin mata a jihar Kano mun dunƙule waje guda domin nuna goyon bayanmu a gareta”

Hajiya Amina Nassarawa da Hajiya Lami Kura kuwa nuna jin dadinsu su ka yi akan yadda Hajiya Maryam ɗin ta himmatu wajen kyautatawa ƴan jam’iyyar APC a jihar Kano, musamman mata da kuma ƴan jam’iyya na ƙasa da ke taka rawa wajen cigaban jam’iyyar.

Hajiya Maryam Kofar Mata da wasu daga cikin magoya bayanta

Ita kuwa Hajiya Sumayya Dala kira ta yi ga gwamnatin jihar Kano da cewa tafiyar A.A Zaura ita ce ra’ayin mafi yawan al’ummar jihar Kano. Haka kuma ta buƙaci shugabacin jam’iyyar APC da dukkanin masu ruwa da tsaki da su marawa Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura baya a takarar gwamnan jihar Kano da ya ke yi a jam’iyyar bisa ga cancanta da kwarewar da yake da ita wajen haɗa kan ƴan jam’iyyar daga kowanne ɓangaren al’ummar jihar.

A nata ɓangaren Hajiya Maryam Umar Kofar Mata godewa wakilan ƙungiyoyin matan ta yi bisa wannan ziyarar goyon baya da su ka kawo mata akan tafiyar A.A Zaura, tare kuma da buƙatar shugabannin kungiyoyin matan da su cigaba da wayar da kan al’ummar jihar Kano akan irin ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ke yi a birni da karkara.

Hajiya Maryam Umar Kofar Mata

Haka kuma ta buƙaci ɗaukacin al’ummar jihar Kano musamman waɗanda shekarunsu su ka kai kuma ba su da katin jefa kuri’a da su hanzarta su yi rijistar domin da ita ne za su samu damar yin zaɓen shekarar 2023.

A ƙarshe Hajiya Maryam Kofar Mata ta godewa ɗaukacin al’ummar jihar Kano musamman mata da matasa bisa irin goyon bayan da su ke bata a harkokin siyasar ta.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan