Adon Furfurar Nasiru Yusuf Gawuna: Tsufa ko Kwalliya?

1215

A ɗan tsakanin nan mataimakin gwamnan jihar Kano kuma tsohon kwamishinan ayyukan aikin gona na jihar Dakta Nasir Yusuf Gawuna ya ɓullo da wani sabon salo a tsakankanin ƴan siyasa ta yadda ya ke barin farin gashi a fuskarsa wanda hakan ke jan hankalin al’umma musamman mata da matasa.

Salon Adon Furfurar da Nasiru Yusuf Gawuna ke yi

Farin gashi da aka fi sani da Furfura da galibi ba a cika samun matasan yan boko ko kuma masu riƙe da shugabanci kan barta ba, sai dai mafi yawan rukunin mutanen da za ka gansu da furfura to babu ko tantama za ka tarar tsofaffi ne da ka iya cewa sun fara fita daga sabgar duniya.

Haka kuma duk da kasancewar tana ɗaya daga cikin baiwar da ubangiji ga yiwa bayinsa ma’ana ba lallai sai mai shekaru akan same shi da Furfurar ba, amma galiban ta kan kasance alama ce ta mutum na da shekaru.

Nasiru Yusuf Gawuna a lokacin yana shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa

Amma salon yadda Nasiru Yusuf Gawuna ke ajiye farin gemu da saje wanda tuni ƴan mata a birnin Kano su ka fara nuna sha’awarsu da wannan sabon salon adon Furfurar mai ƙyalli, wacce aka fi ganin ta a fuskokin tsofaffi. Amma sai ga ta fal a fuskar Gawunan duk da kasancewarsa ɗaya daga cikin matasan ƴan siyasa domin har yanzu bai kai shekaru sittin (60) da haihuwa ba amma kullum fuskarsa cike da furfura wacce ta ke ƙyalli tamkar azurfa.

Nasiru Yusuf Gawuna

Nasiru Gawuna wanda mafi yawan al’ummar jihar Kano ke masa kallon mutum ne mai haƙuri da sauƙin kai da kuma son zaman lafiya da girmama jama’a ya taɓa riƙe mukamin shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa da ke cikin birnin Kano har karo biyu, ya zo da sabon salon da ba a saba ganinsa a tsakankanin ƴan siyasa a jihar ba wato ado da Furfura.

Nasiru Yusuf Gawuna a gurin wani taro ya ke gaisawa da jama’a

Amma ba a za a ce shi ne ya ɓullo da wani ado na daban a tsakanin ƴan siyasar Kanon ba, domin an ga yadda gwamnan jihar Kano na farko a mulkin farar hula, marigayi Muhammad Abubakar Rimi ya yi zamanin adon Falmaran da kuma yadda marigayi Malam Aminu Kano ya yi adon Jar Hula’ da kuma yadda marigayi Aliyu Sabo Bakin Zuwo ya zo da Adon Hular Gashi. Haka shi ma Rabi’u Musa Kwankwaso ya sake dawowa da adon fararen kaya da kuma Jar Hula’.

Nasiru Yusuf Gawuna

Sai dai adon Nasiru Yusuf Gawuna din ya sha bamban da wanda aka saba gani domin na sa na musamman ne la’akari da yadda ya ke barin fuskarsa cike da Furfura mai ƙyalli tare da ɗaukar hankalin wanda su ka yi arba, kuma tuni aka fara samun mukarabbansa da fara kwaikwayon wannan sabon salo.

Abin tambayar shi ne Tsufa ne ko Kwalliya ta saka Gawunan ke ajiye wannan Furfura mai ƙyalli da ɗaukar hankali?

Turawa Abokai

1 Sako

  1. Assalamu alaikum. Al ‘ada ce ta Yan siyasa suna so su zama (unique) wato dabam a cikin jamaa saboda duk inda aka je a gane su. Misali kamar yadda aka Fadi ABUBAKAR Rimi, Sabo bakin zuwo, kwankwaso da sauran su. Marigayi tsohon shugaban kasa Shagari ma haka ya Yi yayin sa na sa doguwar hula zanna ba bu kari

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan