Auren Malala Yousafzai ya yi sanadin jefa wani matashi cikin tsaka mai wuya a Kano

327

Jami’an tsaron hukumar farin kaya na Najert SSS, sun kama wani matashi mai amfani da kafar facebook, Ibrahim Sarki Abdullahi sakamakon tsokanar ƴar gwagwarmayar nan mai rajin kare haƙƙin mata, Zainab Naseer Ahmed a kan ra’ayinta kan aure.

Wata majiya daga hukumar ta bayyanawa jaridar DAILY NIGERIAN cewa Ibrahim Sarki Abdullahi na nan ya na shan tuhuma a kan yadda ya ke tsokanar mutane a kafar sadarwa.

Tun a baya ne dai Zainab ta taɓa bayyana matsayinta a kan aure, in da ta ce “aure ba nasara ba ne”, batun da ya haifar da cecekuce a kafafen sadarwa.

Zainab Naseer Ahmed da Ibrahim Sarki Abdullahi

Haka-zalika a ranar da Malala Yousafzai ta baiyana yin aurenta, jama’a da yawa sun tuna Zainab a kan matsayinta kan aure.

Idan za a tuna, a kwanannan ne dai Abdullahi Ibrahim Sarki ya wallafa hoton Zainab ɗin a facebook tare da wani saƙo da ya ke cewa “Malala ta shushe mu”, lamarin da ya kufular da ƴar rajin kare haƙƙin mata ɗin har ta yi barazanar maka shi a kotu.

Amma daga bayan, bayan Zainab ta yi barazanar maka shi a kotu, sai Abdullahi ya yi wuf ya goge saƙon, amma ina, haƙar shi ba ta cimma ruwa ba, don tuni jami’an farin kaya su ka cafke shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan