Tsohon Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya a majalisar Dattawa ta kasa da ta shude, Kabiru Marafa yayi barazanar kai kwamitin riko na Jam’iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni kara gaban kotu, yana mai bayanin cewar karya kundin tsarin Jam’iyya ne da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya a kyale Gwamna Mai Mala ya cigaba da jan ragamar Jam’iyyar.
Kabiru Marafa yana wannan jawabin ne bayan da Sakataren Jam’iyyar APC na kasa John James yayi barazanar korarsa daga Jam’iyyar, bayan da Sanatan yayi barazanar kafa shugabancin Jam’iyyar a jihar Zamfara.
A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Laraba. Sanata Kabiru Marafa ya bayyana cewar abin dariya ne ma kokarin da kwamitin riko na Jam’iyyar yake yi na ganin ya kore ni. A cewarsa.
Ya kara da cewar, matukar APC ta kore ni to zata auka cikin rikici mai muni wanda ba a taba ganin irinsa ba. A saboda haka Sanata Marafa shima yayi barazanar kai kwamitin riko na Jam’iyyar APC din gaban kotu, domin a cewarsa haramtaccen shugabanci suke yi.