Hotunan yadda ake ɗaukar zango na huɗu na shirin gidan Badamasi wanda shiri ne na barkwanci wanda ya ɗauki hankalin al’umma musamman masu kallo fina-finan Hausa.
Gidan Badamasi labari ne na wani Alhajin Birni da ya yi yawon duniya, wanda cire hula ya fi masa wahala a kan sauya mata.

Ko da yake a gwanancewa da kwarewa ta marubucin bai hasko yawan aure auren da ya yi ba, amma yawan yaransa da kuma dan furucin da ‘yan wasan kan furta shi ya nuna yawan auri sakin da ya yi duk da ba a fadi adadi ba.
Alhaji Badamasi ya tara kudin da har yanzu a zaren tafiyar labarin ba a san adadinsu ba.
Sannan ya tara yara marasa tarbiyyar da fatansu da burinsu shi ne ya rasu domin su mallaki dukiyar da ya tara.

Shirin kunshe yake da kwararru kuma gogaggun ‘yan wasan da suka hada da
Nura Dandolo, Magaji Mijinyawa, Hadiza Gabon Mustapha Naburaska, Sani DanGwari, Umma Shehu, Falalu A. Dorayi, Hadiza Kabara, Tijjani Asase da sauran su.
Tarbiyyar da ba su samu ba ya sa suka shiga kulle-kullen yadda za su sami dukiyar mahaifinsu ta kowace hanya.

Babu jin kai irin wanda ake samu tsakanin ‘Da da Mahaifi ko tausayawar da Soyayya da ake samu Tsakanin Mahaifi da ‘Da.

Da dama suna kallon shirin Gidan Badamasi a matsayin shiri na nishadantarwa, amma ga dukkan mai hange da nazari ya san fim din kunshe yake da ilimantarwa da fadakarwa da nusarwa bisa mummunar rayuwar rashin zabarwa ‘ya’ya uwa tagari da kuma illar rashin tarbiyyantar da ‘ya’yan.