A yammacin yau Alhamis shafukan sadarwa na zamani musamman Facebook su ka cika da labarin rasuwar Sani Abdullahi Ruba, inda ƴan uwa da abokan arziki ke bayyana rashin a matsayin babban rashin da za a dade ba a manta da shi ba.
A shafin sada zumunta na Facebook, jama’a da dama na ci gaba da ta’aziyya da nuna alhini bisa ga rashin mamacin, inda da dama ke bayyana cewa an yi babban rashi.
Sani Abdullahi Ruba ya rasu ne a yau Alhamis sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyarsa ta zuwa Yola da ke jihar Adamawa daga Jos.
Jim kaɗan da faruwar hatsarin a garin Kaltungo da ke jihar Gombe, an garzaya da su cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Gombe domin ceton lafiyarsu, amma rai ya yi halinsa.
Jaridar Labarai24 ta tattaro wasu daga ta’aziyyar da ƴan uwa da abokan arziki ke yi a shafin Facebook.
“Allah ya gafarta ma ka Sani Ruba. Tabbas mutumin kirki ya rasu, a kowanne lokaci ba shi da burin da ya wuce ya ga an taimaki al’umma, ga zamunci, ga amana da cika alkawari. Wallahi ban san komai akan sa ba sai alkhairi, mutunci da kuma girmama juna. Wallahi kai nagari ne. Sani Ruba Allah ya gafartamaka, Allah ya sadaka da rahama” In ji Nura Jos.

Shi kuwa Usman Ja’afar ta’aziyyar ya yi kamar haka “Inna Iillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un! Abinda Allah ya bayar na shi ne, wanda ya karba ma na shi ne, kuma kowanne ya na da kayyadedden lokaci a wajen Allah”.
“Cikin alhini da tsananin kaduwa, na samu labarin rasuwan dan uwanmu, abokinmu Sani Ruba, wanda Allah ya karbi rayuwarsa a yammacin yau“.
“Marigayi Sani mutumin kirki ne wanda yayi rayuwa abin koyi ga na baya, ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa alumma. Tabbas rasuwar wannan saurayi babban rashi ne garemu baki daya. A madadin ni kaina da iyalaina, ina mika ta’aziyyarmu ga iyalai da ƴan uwan wannan bawan Allah da sauran jama’ar jihar Plateau baki daya. Ina rokon Allah SWT ya jikansa, ya gafarta masa, ya sa Aljannah Firdausi ce makomarsa. Ameen”.

Shi kuwa Nasiru Aliyu Gwaram cewa ya yi “Allahu Akbar kabiran Abokin karatu na a Jami’a Mal. Sani Ruba Ya rigamu gidan gaskiya mu sa ka shi a adduar Neman rahama“.
Sani Abdullahi Ruba dai tsohon dalibi ne a tsangayar koyar da aikin jarida da nazarin harkokin sadarwa ta jami’ar Bayero da ke Kano. Haka kuma ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren ƙungiyar ɗalibai na jami’ar ta Bayero.
Hadura a hanyoyin mota dai a cewar masana na daga cikin abubuwa da suka fi haddasa hasarar rayuka da jikkatar mutane a Nijeriya. Galibi ana dora laifin ne a kan rashin kyauwun hanyoyin mota da lafta kayayyaki ko fasinjoji fiye da kima, da rashin cikakkiyar lafiyar ababan hawan, da tukin ganganci da kuma yin karan tsaye ga dokokin hanya baki daya.
A gobe juma’a dai ake sa ran za a yi jana’izar marigayi Sani Abdullahi Ruba a gidansu da ke unguwar Dutse Uku a birnin Jos da ke jihar Plateau.
Munyi Rashin Aboki nagari, Mai San Jama’a Mai kyautatawa kowa Mai zumunchi da Alkairi Allah yagafarta masa yasa Aljannace makomarka.