Rashin bin ƙa’idoji da lalacewar hanyoyi na daga cikin dalilan afkuwar haɗura a Najeriya – Bukarti

170

Barista Audu Bulama Bukarti, mai bincike kan harkokin tsaro a cibiyar Tony Blair Institute da ke ƙasar Burtaniya ya bayyana cewa rashin bin ka’ida da kuma lalacewar hanyoyi a Najeriya na daga cikin manyan dalilan da kan haddasa haɗarin da ake yawaitar samunsa a ƙasar nan.

Audu Bulama Bukarti wanda gogaggyen lauya ne ɗan asalin jihar Yobe, ya bayyana hakan ne a yau Juma’a a shafinsa na Facebook.

Wato yawan mutanen da ke mutuwa a Najeriya dalilin accident, abin akwai tada hankali. Kuma ga shi ba ma tattauna matsalar ma sosai da nufin samo bakin zaren. Kawai sai mu ce kaddara ce, shi ke nan”.

Akwai ƙaddara amma idan muka lura za mu ga cewa akwai sabuba irinsu ganganci da rashin bin ka’idoji da lalacewar hanyoyi. Wadannan ba Allah ne ya daura mana su ba, mu muka jaza wa kanmu su. Idan muka gyara, Allah zai ba mu sauki”. In ji Barista Audu Bulama Bukarti.

84

Wannan dai yana zuwa ne kwana ɗaya da kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Gombe, Ishaku Gabmi Ibrahim, ya bayyana cewa kimanin mutane 84 ne suka mutu a hatsarin mota 350, wasu 939 kuma suka samu munanan raunuka daga watan Janairu zuwa Nuwamban shekarar 2021 a Jihar Gombe.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), ya bayyana hakan ne a rahoton wata kididddigar da hukumar ta fitar ranar Alhamis.

Haɗura dai a hanyoyin mota dai a cewar masana na daga cikin abubuwa da suka fi haddasa hasarar rayuka da jikkatar mutane a Nijeriya. Galibi ana dora laifin ne a kan rashin kyauwun hanyoyin mota da lafta kayayyaki ko fasinjoji fiye da kima, da rashin cikakkiyar lafiyar ababan hawan, da tukin ganganci da kuma yin karan tsaye ga dokokin hanya baki daya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan