Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya cika shekaru 64 da haihuwa

515

An haifi Dr. Goodluck Ebele Jonathan ne a ranar 20 ga watan Nuwambar shekarar 1957 kimanin shekaru 64 da su ka gabata a garin Otueke na karamar hukumar Ogbia da ke a wancan lokacin yankin gabashin Najeriya, yanzu kuma yake jihar Bayelsa.

Sana’ar iyayensa ita ce sassaka jirgin ruwa watau kwale-kwale.

Ya yi karatun digirinsa na farko a fannin ilimin dabbobi, sannan kuma ya yi digirinsa na biyu a fannin ilimin halittun ruwa a yayin da ya samu digirin digirgir a fannin ilimin dabbobi a jami’ar Fatakwal.

Bayan da ya samu digirinsa na farko, ya yi aiki a matsayin sifeton da ke sa ido kan yadda malamai suke gudanar da ayyukansu, sannan kuma ya yi malamin jami’a da kuma jami’in da ke sa ido kan kare muhalli, aikin da yake yi har zuwa lokacin da ya shiga siyasa.

A shekarar 1998 ne, Dr. Goodluck Jonathan ya fara shiga al’amuran siyasa, inda ya shiga jam’iyyar PDP.

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan

Ya zama mataimakin gwamnan jihar Bayelsa a shekarar 1999 bayan da Diepreye Alamieyesegha ya lashe zaben gwamnan jihar karkashin tutar jam’iyyar PDP.

Dr Goodlck Jonathan ya zamo gwamnan jihar Bayelsa bayan da majalisar dokokin jihar ta tsige Alamieyesegha bisa zargin kokarin hallata kudin haram a Biritaniya da kuma almundahana da dukiyar jama’a.

Lokacin yana mataimakin shugaban Najeriya

A shekara ta 2006, an zabi Dr. Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa, kuma bayan zaben da aka yi a shekara ta 2007 an rantsar da shi a matsayin mataimakin shugaba Umaru Musa ‘Yar Adua.

Bayan rasuwar shugaban Najeriya, Umaru Musa ‘Yar Adua sakamakon doguwar jinya, sai aka rantsar da Goodluck Jonathan a matsayin shugaban Najeriya kuma babban kwamandan askarawan kasar.

Lokacin yana shugaban ƙasa

A shekara ta 2011 ya lashe zaben shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP tare da mataimakinsa Muhammed Namadi Sambo.

A karshen shekara ta 2014 kuma ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zabukan 2015.

Dr. Goodluck Jonathan na da mata daya Dame Patience Jonathan da ‘ya’ya biyu.

Jonathan shi da mai ɗakinsa
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan