Gwamnatocin da su ka gabata ne silar matsalar ruwan sha a Kano – Ganduje

199

Gwamnatin Jihar Kano ta ɗora alhakin matsalar ruwan sha da ke samun jihar a kan gwamnatocin baya.

Kwamishinan albarkatun ruwa, Sadiq Aminu Wali ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin.

Kwamishinan ya ce ƙalubalen ƙarancin ruwan sha da ake fama da shi a wasu yankunan jihar matsala ce da ake danganta ta da al’amura da dama da aka gada daga gwamnatocin da suka gabata a jihar.

Wali ya baiyana cewa ɗaya da ga cikin manya-manyan dalilan da su ka haifar da ƙarancin ruwa a Kano sun haɗa da yawan al’umma, lalacewar bututun da a ka gada daga gwamnatocin baya, da kuma amfani da na’urorin da ba su da inganci daga cikin kamfanonin sarrafa ruwa da dai sauransu.

“Tun zuwan gwamnatin jihar Kano ta dauki matakan shawo kan wannan kalubale, mun gana da hukumomin bayar da tallafi da kuma wata Hukuma daga Kasar Faransa don gyaran manyan cibiyoyin ruwa guda biyu a cikin birnin Kano na Challawa da Tamburawa” inji Wali

Kwamishinan ya gwamnatin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ɗauki kwararan matakai na magance matsalar karancin ruwan sha a jihar Kano Baki daya.

Ya ce gwamnatin za ta gudanar da gyararraki a manyan madatsun ruwa guda biyu da su ka haɗa da gyaran kayiyyakin tunkuɗo ruwa, bututu, da mitoci, da faɗaɗa wasu ƙananan madatsun a ƙananan hukumomin jihar.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, idan aka kammala gyaran, matsalar ƙarancin ruwa za ta zama tarihin a Kano.

Wali ya danganta wasu daga cikin manya-manyan abubuwan da ke haifar da karancin ruwa da rashin isashshiyar wutar lantarki, yana mai jaddada cewa idan babu isasshiyar wutar lantarki akai-akai famfunan ruwa ba za su iya fitar da ruwan ta cikin bututun ga jama’a yadda ya kamata ba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan