Ranar yaƙi da cin zarafin mata ta duniya

142

Majalisar Dinkin Duniya ta keɓe ranar 25 ga watan Nuwamban kowacce shekara domin tunawa da matsalar cin zarafin mata a ƙasashen duniya.

A cewar Majalisar matsalar babban ce a tsakanin al’umomi daban-daban na duniya, da ke tauye ƴancin mata ta fuskar ilimi da kiwon lafiya da tattalin arziki da kuma zamantakewa.

A Najeriya masu fafutukar kare hakkin bil’adama da hana cin zarafin mata sun nuna damuwa game da yadda matsalar fyade take karuwa a kasar nan.

Kuma sun bayyana damuwa game da matsalar fyade da kuma yadda ake sace mata da kuma ‘yan mata musamman a yankin arewa-maso-gabas da arewa ta tsakiya da kuma wasu jihohi a yankin Arewa maso yammacin ƙasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan